1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya za ta mika takaddun fita daga EU

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 29, 2017

A wannan Larabar Firaministar Birtaniya Theresa May za ta mika takaddun fara aiwatar da kammala fitar kasarta daga cikin kungiyar Tarayyar Turai EU a hukumance.

https://p.dw.com/p/2aBxm
Firaministan BirtaniyaTheresa May na sanya hannu kan takaddun fita daga EU
Firaministan BirtaniyaTheresa May na sanya hannu kan takaddun fita daga EUHoto: REUTERS/C. Furlong

Wannan dai shi ne karo na farko da wata kasa daga cikin kasashe mambobin kungiyar 28 ke fice wa daga EU din, inda a yanzu ya rage sauran kasashe 27 a cikinta. Za dai ta sanya hannu kan wannan yarjejeniyar mai dinbin tarihi a fadar gwamnatin Birtaniyan da ke Downing Street, inda daga bisani jakadan kungiyar EU din a Birtaniya Tim Barrow zai mika ta ga shugaban kungiyar Donald Tusk. A karkashin kundin dokokin kungiyar na Article 50 dai, tilas ne duk kasar da ke son fita daga EU ta tatauna batun ficewarta daga kungiyar har na tsahon shekaru biyu.