1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya zata janye ƙarin dakarunta daga Iraƙi a farkon shekara mai zuwa

October 8, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8w

FM Birtaniya Gordon Brown ya ce gwamnatinsa zata rage yawan dakarun kasar a Iraqi zuwa dubu 2 da 500 a farkon sabuwar shekara. FM yayi nunar da haka ne a wani jawabi da yayi a gaban majalisar dokoki dake birnin London. Hakan ya zo ne mako guda bayan da yayi alkawarin rage yawan dakarun Birtaniya a Iraqi ya zuwa dubu 4 da 500 kafin karshen wannan shekara.

Brown ya ce “Muna shirin rage yawan dakarun mu a kudancin Iraqi zuwa dubu 2 da 500. An fara mataki na farko inda yanzu haka ´yan Iraqi suka karbi ragamar tabbabar da tsaro.”

Da farko FM na Birtaniya ya fadawa wani taron manema labarai cewa ba zai iya kawad da duk wani mataki da za´a iya dauka a dangane da fito na fito da ake yi tsakanin kasashen yamma da Iran akan shirinta na nukilyia ba. To amma a lokaci daya ya ce yayi imani za´a iya warware wannan takaddama a diplomasiyance.