1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bobs 2016: Wasu 'yan Indiya sun yi nasara

Gazali Abdou TasawaMay 2, 2016

Masu fafutuka wajen kawar da kai hari kan mutane da ruwan guba ko Acid a Indiya sun samu lambar yabo ta Bobs ta DW ta wannan shekara ta 2016

https://p.dw.com/p/1IgP2
Opfer von Säureattacken Tuba und Rupa
Hoto: Anurag Dwivedi

Yawan mutanen da aka kai wa hari da ruwan Acid a kasar Indiya ya karu da kashi 250 daga cikin dari daga shekara ta 2012 zuwa ta 2014. Akasarin wadanda lamarin ke shafa mata ne wadanda ruwan Acide din ke lalata masu fuska.

Wannan ce ta sanya hukumomin kasar ta Indiya suka kaddamar da wani kampe na neman kawar da wannan muguwar tabi'a ta kai hari da ruwan acide da aka yi wa lakabi "Stop Acid Attacks" ta hanyar faya-fayen bidiyo masu nuna fuskokin mutanen da aka kaiwa hari da ruwan na Acid.

Kampe din ya samu karbuwa kwarai a gurin al'umma tare da yin tasiri sosai wajen fadakar da su kan illar abin da muhimmancin yin watsi da tabi'ar harar mutanen da ruwan na Acid. Wannan kamfe na "Stop Acid Attacks" ya samu lambar yabo ta Bobs ta 2016 a fannin rawar da aikin jarida ke takawa wajen sauya tunanin al'umma.