1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram: Mun sake kwace Bosso na NIjar

Abdul-raheem Hassan/ MABJune 6, 2016

A karo na biyu cikin kwanaki hudun da suka gabata, kungiyar Boko Haram da ke fafutuka da makamai ta mayar da garin Bosso na Jamhuriyar Nijar karkashin ikonta.

https://p.dw.com/p/1J1Y1
Nigeria Boko Haram Terrorist
Hoto: picture alliance/AP Photo

Kungiyar Boko Haram ta sake karbar iko da garin Bosso da ke yankin Kudu maso Gabashin Jamhuriyar Nijar, bayan kazamin fada da aka gwabza tsakanin sassa biyu. Magajin garin Bosso da kuma wata kafar sojoji sun tabbatar da wannan labarin, inda suka ce dakarun Najeriya da Nijar sunyi artabu da mayakan na Boko Haram a daren jiya Lahadi zuwa safiyar wannan Litinin.

A ranar Jumma'a da ta gabata ne dai tsagerun na Boko Haram suka fara kwace garin na Bosso daga hannu Sojin Nijar bayan da suka kashe dakaru 30. Sannan manyan jamio'an sojin Najeriya biyu sun rigamu gidan gaskiya a wannan gumurzu. Bosso na Nijar da ke kan iyakam da Najeriya ya saba fusakntar hare-haren ta'addanci tun bayan da 'yan gudun hijira suka samu mafaka a garin.