1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta sace ma'aikatan Kamfanin mai 10

Ramatu Garba Baba MNA
July 26, 2017

Kamfanin mai a Najeriya ya zargi mayakan kungiyar Boko Haram da sace masa ma'aikata goma da ke gudanar da aikin bincike a jihar Borno.

https://p.dw.com/p/2hBfW
Nigeria Boko Haram Terrorist
Hoto: picture alliance/AP Photo

Kamfanin mai a Najeriya ya ce an sace masa ma'aikata goma da ke gudanar da aikin binciken a jihar Borno a Arewa maso Gabashin kasar, ana dai zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne suka yi awon gaba da Masanan da suka shafe shekaru suna bincike kan albarkatun Mai a yankin tafkin Chadi, rahotanni daga kasar na cewa mayakan sun yi nasarar yin garkuwa da mutanen a yayin musayar wutar da ta auku a tsakanin jami'an tsaro da ke rakiyar tawagar da mayakan a kusa da wani kauye mai suna Jibi a jihar Borno.

Wasu da suka tsira daga gumurzun sun shaida wa manema labarai a Maiduguri cewa 'yan bindigar sun bude wa ayarinsu wuta inda ake fargabar wasu ciki har da jami'an tsaron sun rasa ransu. Bayan da aka yi ta yada jita-jita kan harin, kamfanin man na kasar NNPC ya fito ya tabbatar da cewa, hakika an kame wasu ma'aikatansa guda goma tare da cewa masana na yankin ne inda suke gudanar da aikin bincike kan tarin albarkatun mai na yankin tafkin Chadi. Wannan ba shi ba ne karon farko da kungiyar ke yin garkuwa da ma'aikata don ko a watan Yunin da ya gabata ma, Boko Haram ta yi garkuwa da wasu mata goma wadanda jami'an tsaro ne da ke kan hanyarsu ta zuwa garin Damboa a jihar ta Borno.