1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haramun a Bauchi

September 8, 2010

'Yan ƙungiyar Boko Haramun sun kai hari a Bauchi, inda suka saki fursunoni kimanin 800, a gidan yari.

https://p.dw.com/p/P6uV
'Yan Boko Haram da aka kama baraHoto: AP

Wasu da ake zargin cewa 'yan ƙungiyar Boko Haramun ne sun kai hari a gidan yarin Bauchi. Inda suka yi bata kashi da jami'an tsaro. Kwamishinan 'yan sanda na jahar Bauchi Alhaji Danlami Danbaba Yar'aduwa ya shaidawa Deutsche Welle cewa, yayin musayar wutan an kashe soja ɗaya da ɗan sanda da wasu fararen hula. An kuma rauna ta mutane dayawa ciki har da ma'aikatan gidan yarin. Ana dai zaton cewa 'yan ƙungiyar Boko Haram da aka fatattaka a barane suka kai harin don kuɓutar da 'yan uwansu dake ɗaure. Kwamishina 'yan sanda yace masu bindigan sun saki mutane fiye da 721 dake gidan yarin. Wannan 'yan ƙungiyar dai sun isa gidan yarin suna ta kabbara kafin aji harbe-harbe. Rohotonni daga birnin na Bauchi suka ce 'yan sanda da sojoji sunyi ta harbi kan iska, abinda kuma ya watsa 'yan ƙungiyar. Yanzu dai komi ya lafa a birnin na Bauchi inda jami'an tsaro ke ta sintiri.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu