1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boren kin jinin shugabar Koriya ta Kudu

November 19, 2016

Badakalar cin hanci ta shafa wa Shugaba Perk Geun-Hye ta Koriya ta Kudu kashin kaji. Saboda haka ne al'ummar kasar suka gudanar da gagarumin maci don neman ta sauka daga kujerarta.

https://p.dw.com/p/2Swa2
Südkorea Massenproteste in Seoul gegen Präsidentin Park Geun Hye
Hoto: Reuters/K. Hong-Ji

Dubun-dubatar 'yan Koriya ta Kudu sun sake fitowa kan tituna a mako na hudu a jere, domin neman shugabar kasa Park Geun-Hye ta sauka daga karagar mulki sakamakon badakalar cin hanci da ta shafeta. Rabon wannan kasa ta Asiya ta fuskanci irin wannan fushi na al'umma tun shekaru 36 da suka gabata.

Wadanda suka shirya wannan bore sun ce mutane dubu 300 ne suka amsa kira, yayin da 'yan sanda suka ce yawan mutanen ba su fi dubu 70 ba. Daliban sekandare ma sun shiga an dama da su a zanga-zangar, bayan da suka kammala jarrabawar shiga jami'a.

Wata aminiyar Shugaba Park Geun-Hye ce ta shafa mata kashin kaji, sakamakon amfani da hanyoyin da ba su dace ba wajen samun tallafi mai tsoka daga kanfanonin kasar, tare da zurawa a aljuhunta. Duk da cewa shugabar ta Koriya ta Kudu ta nemi gafara game da wannan batu, amma kuma 'yan adawa na ci gaba da zarginta da sakaci da nuna sonkai.