1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boren `Yan adawa a Georgia ya fara lafawa

Ibrahim SaniNovember 8, 2007
https://p.dw.com/p/C5bW

Rahotanni daga birnin Tbilisi babban birnin kasar Georgia, na nuni da cewa al´amurran boren ´Yan adawa ya fara lafawa. Hakan a cewar bayanai, ba zai rasa nasaba da ingantattun matakan tsaro ne da yan sandan kasar suka dauka ba,musanmamma a babban birnin ƙasar.A yanzu haka dai dokar ta ɓaci da shugaba Mikhail Saakashvili ya kafa na nan na aiki, a faɗin kasar baki ɗaya.Shugaban dai ya kafa wannan dokar ne, a sakamakon zanga zangar adawa da aka gudanar ne a kasar har na tsawon mako guda.Jami´an kiwon lafiya na kasar sun tabbatar da cewa mutane sama da ɗari 5 ne suka jikkata a zanga zangar jiya, bayan da ´Yan sanda suka harba musu barkokon tsuhuwa da kuma harsashai na robobi.