1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Borno: An kafa dokar kula da masu wa'azi

Al-Amin MohammedAugust 12, 2016

Gwamnatin Borno ta dauki wannan mataki ne bisa la'akari karuwar gurbatattun ra'ayoyi da ke haifar da rashin fahimta tsakanin mabiya addinai da sakarwa harkokin addinan mara.

https://p.dw.com/p/1JhOk
National Mosque in Abuja, Nigeria
Hoto: DW

Kazalika da yadda aka sakewa al'umma mara wajen yin karance-karance ba tare da sanya dokoki ko ka'aidoji da ke tabbatar da sai wanda malamai suka amince malami ne kafin ya karantar da mutane ko yin wa'azi ba.Bisa wannan dalili ne da kuma kokarin rage koyar da tsatsauran ra'ayi tsakanin matasa ya sa gwamnatin jihar Borno ta kafa wata hukumar malaman addinin musulunci da za su ke sa ido kan ayyukan malamai masu wa'azi a yankunan kananan hukumomi 27 da ke jihar.


Wannan hukuma dai an dora ma ta alhakin tantance masu wa'azi da koyarwa a masallatai da kuma tura wasu mutane masu leken asiri zuwa garuruwa da kauyuka domin jin irin hudubar da malamai ke yi a masallatan Juma'a da makarantu don gano masu koyar da tsattsauran ra'ayi.Gwamnan jihar Borno Kashim Shatima wanda ya kaddamar da wannan hukuma da ta kunshi malaman addinin musulunci, ya ce gwamnatin sa ta dauki wannan mataki ne domin dakile yaduwar tsattsauran ra'ayi wanda ya kai ga haifar da Kungiyar Boko Haram.


Tuni dai bangarorin al'umma suka fara tofa albarkacin bakin su kan muhummancin kafa wannan hukuma da ma yadda ya kamata hukumar ta gudanar da ayyukan ta.
Sayyid Murtala Sheikh Abul Fatahi wani malamin addainin musulunci ne Maiduguri ya shaida min ta wayar tarho cewa sun gamsu da kafa matukar za'a bar hukumar ta yi aiki kuma gwamnati zata yi amfani da shawarwarin da ta ke bayarwa.