1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Borno: Bincike kan kwashe abincin 'yan gudun hijira

Al-Amin Sulaiman Muhammad/ASSeptember 16, 2016

Majalisar wakilan Najeriya ta ce za ta gaggauta gudanar da bincike kan yadda ake karkata kayan abinci da ake kai wa ‘yan gudun hijira a Maiduguri.

https://p.dw.com/p/1K3kp
Symbolbild Nigeria Bama Flüchtlinge
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Ola

'Yan gudun hijira dai musamman a Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno na ci gaba da fuskantar karancin abinci inda suke bayyanan cewa wasu da dama na mutuwa musamman yara da mata saboda yunwa. Wannan hali da suke ciki ya sanya su yanke hukuncin yin zanga-zanga don jan hankalin hukumomi kan wannan batu.

Ana dai alakanta halin da ‘yan gudun hijirar ke ciki da yadda ake karkatar da kayan abinci na agaji da gwamnatin tarayya ta ke aike musu da shi da kuma wanda kungiyoyin da daidaikun mutane ke kaiwa. Hon. Yakubu Dogara da ke zaman kakakin majalisar ta wakilan Najeriya ya shaida min cewa za su fadada binciken har kan kudaden da ake aikowa na taimako 'yan gudun hijira wanda ba su san inda suke shiga ba.

Shi ma mataimakin shugaban kwamitin kula da agajin gaggawa na majalisar wakilan Hon. Ali Isa JC ya ce masajalisar fa ba za ta bar duk wanda aka samu da hannu a karkatar da kayan agaji da ake aikewa 'yan gudun hijirar ba. Sai dai kungiyoyin kare hakkin bani Adama sun ce ba yin binciken ba aiwatar da sakamakon da ke kunshe a ciki shi ne abinda kowa ya fi so domin a baya ma gwamnatin tarayya da ta Borno sun gudanar da binciken amma ya zuwa yanzu ba a fitar da sakamakon bincike ba kuma babu wani da aka ji an hukunta a kan wannan zargi.

Nigeria Stadt Borno State
Dubban 'yan gudun hijira ciki har da tsofaffi da yara ne ke fama da yunwa saboda karancin abinciHoto: Getty Images/AFP/Stringer