1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Britania zata tura karin dakaru a Afganistan

February 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuSc

Britania ta sanar dacewa zata aike da karin dakarun soji 800 zuwa kudancin Afganistan,adadin dayake kalilan koda yake zai taimakawa ayarin dakarun tsaro na NATO,dake cigaba da fuskantar yan adawa a wannan kasa.Wannan sabuwar sanarwa daga Britania dai na nuna alamun cewa kungiyar tsaron ta NATO ,na dada zage dantse wajen kalubalantar mayakan Taliban,musamman da rani.Ayarin dakarun kasa da kasa a karkashin jagorancin NATO ,da yawansu yakai dubu 30 ne ahalin yanzu ke ke taimakawa gwamnatin shugaba Hamid Kharzai ,bayan kifar da gwamnatin yan taliban masu tsattsauran raayi.A yan lokutan da suka gabata dai,mayakan taliban din sun dada karfafa hare haren da suke kaiw