1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan gudun hijira dubu 5,000 yan kasar Syriya

Kamaluddeen SaniSeptember 4, 2015

Prime ministan kasar Britaniya David Cameron ya bayyana cewar Britaniya zata kara karbar Karin dubban yan gudun hijira daga kasar Syriya.

https://p.dw.com/p/1GRDA
David Cameron
Prime minstan Britaniya David CameronHoto: Reuters/T. Melville

David Cameron ya bayyana hakan ne ga manema labarai a birnin Lisbon na kasar Potugal bayan ya gana da mahukuntan kasar, a inda ya kara da cewar tuni Britaniyan ta karbi 'yan gudun hijirar kasar Siriya dubu 5,000 a karkashin jadawalin shirin mutsugunar da yan gudun hijirah kuma za su cigaba da yin maraba da yan gudun hijirar.

Shugaba Cameron ya ce yanayin girman matsalar da kuma wahalhalun da 'yan gudun hijirar suke fuskanta ne ya sanya dole su yi duk abin da ya dace don kara tsugunar da 'yan gudun hijirar Siriya a kasar ta Britaniya.