1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brown zai yi murabus

Usman ShehuMay 11, 2010

Firimiyan Birtaniya ya bada sanarwa zayyi murabus daga shugabancin jam'iyarsa ta Labour bayan kayen da ya sha a zaɓe

https://p.dw.com/p/NLQ3
Gordon BrownHoto: AP

Firayim minista Gordon Brown ya sanar da yin murabus ɗin ne, domin bada damar kafa gwamnatin haɗaka da jam'iyar Liberal Demokirat ta masu sassaucin ra'ayi. Ci gaba da kasancewar Brown a kan shugabancin jam'iyar, abune da ake ganin zai iya kawo tarnaƙi a ƙoƙarin da Jam'iyar sa ta Labour ke yi, na samun goyon bayan jam'iyar Liberal Demokrat. Wannan mataki da Firayim ministan ya ɗauka, ana ganin ya sanya jam'iyar Conservative cikin wani hali na kota amince ta kulla ƙawance da Liberals, domin kafa gwamnati, ko kuma ta ci gaba da zama jam'iyar adawa. Tuni dai jam'iyar ta Conservative ta ce za ta duba buƙatun Liberals Demokrat, waɗan da suka haɗa da batun yin gyara a dokar zaɓen ƙasar ta  Birtaniya. zaɓen da mutane da dama suka yi kukan cewa basu samu daman kaɗa ƙuri'u ba.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu