1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buƙatar hana killace Gaza

June 3, 2010

Duniya na ƙara matsawa Isra'ila da lallai sai ta kawar da killace Gaza da take yi

https://p.dw.com/p/NgLC
Tutar neman buɗe zirin GazaHoto: dpa

Ɗaruruwan 'yan fafitika da suke cikin tawagar kai agaji a Gaza wanda Isra'ila ta farma suka dawo ƙasar Turkiyya, wasu jiragen sama ukku ne suka sauka a filin jiragen saman Instanbul ɗauke da 'yan fafitikar wanda Isra'ilan ta sako bayan tsaresu da tayi na kwana ukku. Mutanen dai sun samu gagarumin tarba.

Isra'ilan dai har izuwa wannan lokacin tana ci gaba da samun tofin Allah tsine daga sassa daban daban na duniya. Duk da cewa tun  jiya ta fara sako mutanen, amma ko a yammacin jiyan Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-moon, ya sake jaddada cewa dole ne Isra'ila ta kawo ƙarshen killace yankin Gaza.

 Kakakin gwamnatin Isra'ila Mark Regev ya bayyana dalilan sako mutanen da cewa: Ba mu son tsare masu fafitika a kurkukun Isra'ila, shi yasa muka gaggauta maida su ƙasashensu, kuma muna fatan dukkaninsu su ficce daga ƙasarmu cikin sa'o'i 48.

Ƙasar Turkiyya dai tace ta buƙaci Amirka sai lallai ta tilastawa Isra'ila sako dukkan mutanen, domin bata da ikon hukunta wani da ta kama a tekun ƙasa da ƙasa. Inda ministan harkokin wajen Turkiya Ahmet Davutoglu ya gargaɗi Sakatariyar harakokin waje Amirka da cewa, idan ba'ayi hakan ba abinda zai biyo baya ba mai daɗi bane. 

Tun bayan wannan lamarin dai, Turkiyya sai zafafan kalamai kawai take fitarwa. Ga abinda  Firayim ministan ƙasar Raccep Tayyip Erdogan ya bayyana a zaman Majalisar dokokin ƙasar a jiya:

Erdogan yace wannan zubar da jini da kisan kiyashi wanda Isra'ila ta yi wa masu kai agaji izuwa Gaza, akwai buƙatar a ladabtar da ita. Wannan farmakin na Isra'ila ya saɓawa dokokin ƙasa da ƙasa da yancin bil'adama, dama zaman lafiya a duniya.

A sakamakon wannan abinda Isra'ila ta yi Tarayyar Turai da Rasha da Majalisar Ɗinkin Duniya, duk sun buƙaci sai a gudanar da bincike mai zaman kansa, domin Isra'ila ta taka dokokin duniya. Inda ministan harkokin wajen Jamus Guido westerwelle yace:

Tilas ne a gudanar da bincike mai zaman kansa, kana a kyautata samar da agaji a yankin Gaza, daɗin daɗawama, abinda Kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya zatar aiwatar da shi ya zama dole.

Da yake jawabi kan lamarin Firayim ministan ƙasar bani Yahudu Benjamen Natenyahu, ya kare matakin na Isra'ila inda yace suna da ikon kare kai. To sai dai ita kuwa ƙungiyar da ta jagoranci kai agajin wanda ya samu hallatar 'yan ƙasashe daban daban har 42, tace muddin dai Isra'ila bata kawar da killace yankin Gaza ba, to za ta sake shirya wata gagarumar tawagga, wanda kuma dole sai sun isa Gaza, inda za su bi ta ƙasar Masar, domin a faɗarsa Gaza ta kasance tamkar wani gidan yari.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Yahouza Sadissu Madobi