1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buɗe zaman Majalisar dokokin Zimbabwe

Zainab MohammedAugust 26, 2008

Shugaba Robert Mugabe ya zargi Amurka da Britaniya da yunkurin kifar da gwamnatinsa

https://p.dw.com/p/F58f
Shugaba Robert Mugabe na ZimbabweHoto: AP

Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe ya zargi Britania da Amurka wajen amfani da tashin farashin kayayyakin abincin ƙasar ,wajen yunkurin kifar da gwamnatinsa.

Duk da adawa da 'yan adawa sukayi dashi, Robert Mugabe ya buɗe majalisar dokokin ƙasar yau,inda ya jaddada cewar akwai yiwuwar cimma daidaito wajen kafa gwamnatin haɗaka a wannan ƙasa, wanda keda nufin warware rigingimun sakamakon zaɓe da Zimbabwen ta faɗa ciki.

Sai dai a daidai lokacin da shugaba Mugabe ke jawabinsa na buɗe majalisar,Wakilai daga jami'iyyun adawa sunyi ta yi masa ihu ,wanda ya nuna halin ko oho.

Mai shekaru 84 da haihuwa,shugaban na Zimbabwe yace kawo yanzu an cimma daidaito kan muhimman batutuwa ,da fatan kuma nan bada jimawa ba za a rattaba a hannu akan yarjejeniyar kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa.

Duk da adawa daga wakilan jami'iyyar MDC dangane da bude majalisar ayau,dukkaninsu sunyi dafifi domin marawa ɗaya daga cikinsu baya,wanda aka zaɓa jiya zuwa matsayin kakakin majalisar.

Mai magana da yawun jami'iyyar adawa ta MDC Nelson Chamisa ya bayyan tattaunawar dake gudana da kasancewa wata madafa a yunkurin warware rigingimun siyasar ta Zimbabwe domin samun makoma ta gari....

"Wannan na zama babbar nasara a bangaren Demokradiyya wanda kuma ke bayyana fatan al'ummar wannan kasa na ganin cewar an samu sauyi a harkokin mulkin jamai'iyyar Zanu-Pf,tare da kwato kasar da halin da take ciki.Wanda hakan zai kasance makoma mai kyau wa sanbuwar Zimbabwe,bisa ga kyakkyawan sakamakon tattaunawar"

MDC dai ta bayyana cewar shugaban na Zimbabwe bashi da ikon buɗe majalisar,tare da gargadin cewar yin hakan zai iya dakushe tattaunwar dake gudana tsakanin jami'iyyun dangane da warware rikicin siyara da kasar kudancin Afrikan ke fama dashi.

Kazalika Jami'iyyar Zanu-Pf ta samu matsayin jagorancin majalisar Dottijai inda take da rinjaye,wanda ke tabbatar da hakkin daya rataya a wuyan bangarorin biyu na ganin cewar an cimma yarjejeniyar tsamo Zimbabwe daga halin kuncin rayuwa da take ciki.

Tattaunawar ɓangarorin biyu dai na fuskantar matsaloli ,bayan rushewarsa a baya,dangane da zargin da Jami'iyyar adawa kewa Mugabe na kin ajiye mukaminsa a matsayin shugaban ƙasa,shekaru 28 da kasancewa kan madafan iko.