1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari na tattaunawa kan 'yan matan Chibok

Mouhamadou Awal Balarabe
April 13, 2017

A daidai lokacin da ake cika shekaru uku da garkuwa da 'yan matan Chibok, gwamnati tarayyar Najeriya ta kyautata zato dangane da tattaunawar da take yi da 'yan Boko Haram don ganin sun sakosu.

https://p.dw.com/p/2bCJO
Nigeria Präsident Buhari empfängt befreites Schulmädchen Amina Ali
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa tana ci gaba da tattaunawa da kungiyar Boko Haram don ganin an sako sauran 'yan matan sakandaren Chibok da ake garkuwa da su. Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ne ya yi wannan bayanin a jajiberen cika shekaru uku da sace 'yan mata 276 a wata makarata ta jihar Borno, inda ya ce akwai alamun samun nasara a tattaunawar.

Har yanzu dai 'yan matan Chibok 190 na hannun 'yan Boko Haram.  A ranar 14 ga watan Afirilu 2014 ne, 'yan bindiga suka shiga cikin makarantar kwana ta garin Chibok inda suka yi awon gaba da 'yan matan sakandaren.  Kungiyar bada agaji te Red Croos ko Croix rouge da kuma hukumomin Switzerland sun yin nasarar karbo 20 daga cikin 'yan matan biyo bayan tattaunawa da Boko Haram. Yayin da wasu daga cikin 'yan matan suka samu arcewa.