1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari ya mayar wa mai dakinsa Aisha da martani

October 14, 2016

Shugaban Najeriya ya yi amfani da taron manaima labarai da ya gudanar a Berlin bayan ganawa da ya yi da Angela Merkel wajen bayyana cewar dafa abinci da hidimar gida ne aikin Aisha ba shisshigi a harkokin siyasa ba.

https://p.dw.com/p/2RFvy
Deutschland Berlin - Merkel trifft auf Muhammadu Buhari im Bundeskanzleramt
Hoto: picture-alliance/dpa/R. Jensen

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya mayar wa mai dakinsa da martani dangane da sukar gwamnatinsa da ta yi inda ya ce ba huruminta ba ne. A lokacin da ya amsa tambayar da aka yi masa a birnin Berlin kan hirar da tashar BBC ta yi da Aisha Buhuri, shugaban na Najeriya ya ce dafa abinci ne aikinta, amma ba tsoma baki a harkokin siyasa ba.

Ita dai Aisha Buhari ta yi barazanar kin mara wa mai gidanta baya a zaben 2019 saboda ya yi watsi da galibin wadanda suka taimaka masa darewa kan karagar mulki, inda ta ce da wasu tsageru ne yake dama harkokin mulki. Sai dai shugaba Buhari ya ce ya san abin da yake yi saboda so hudu ya tsaya takarar shugabancin kasa kafin ya yi nasara.

Shugaban Najeriya na ta shan suka dangane da manufofinsa na tattalin arziki saboda komabayan da kasar ke samu sakamakon faduwar farashin man fetur. Muhammadu Buhari da aka zaba a Maris na 2015 ya yi alkawarin yakin da cin hanci da ya hana tattalin arzikin Najeriya mikewa.