1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari zai gana da Trump

April 16, 2018

Gwamnatin Amirka ta ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai ziyaci kasar inda zai gana da shugaba Donald Trump nan gaba kadan a birnin Washington.

https://p.dw.com/p/2w6UF
Muhammadu Buhari Präsident Nigeria Porträt G7 Gipfel 2015 Schloss Elmau
Shugaba Muhammadu Buhari na NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa/Minkoff

Fadar White House ta Amirka, ta ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki a kasar inda zai gana da takwaransa Donald Trump a birnin Washington. A cewar wata sanarwar da ta fitar, fadar ta White House ta ce ganawar shugabannin biyu, wadda za a yi ranar 30 ga wannan watan na Afrilu, za ta tabo batutuwan tattalin arziki da yaki da ta'addanci. Akwai ma batun kyautata tafiyar Najeriya a demokuradiyyance, saboda tasirin kasar a siyasar nahiyar Afirka.

A makon jiya ne dai Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana aniyar sake tsayawa takara a zaben da za a yi a badi, abin kuma da ya sanya wasu ke kiraye-kiraye da kar ya yi hakan. Kasar ta Buhari dai na fuskantar matsalolin tsaro ta fuskoki da dama, duk da damarar da gwamnatinsa ta ja na sama wa lamarin magani.