1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar biyan diyya ga harin Rann

January 24, 2017

Al'ummar yankin Kalabalge da ke jihar Borno da sojojin Najeriya suka yi kuskuren jefawa bama-bamai, sun nemi gwamnatin Najeriyar ta biya su diyya a dai-dai lokacin da alkaluman wadanda suka mutu a hadarin ke karuwa.

https://p.dw.com/p/2WKR4
Nigeria Luftangriff auf Flüchtlingslager
Hoto: Reuters/MSF

Kiraye-kirayen biyan diyya kan harin na makon da ya gabata, ya faro daga kungiyoyin kare hakkin dan Aadam wanda suka ce tunda Gwamnati ta tabbatar da yin kuskuren hallaka mutane to ya zama dole a biya diyya ga wadanda abin ya shafa. Hakan ne ya bai wa al'ummomin wannan yankin damar neman a biya su diyyar mutanen da suka mutu da kuma wadanda suka jikkata kamar yadda daya daga cikin mutanen garin ya bayyana wa wakilin DW  bisa sharadin sakaye sunansa.

Yanzu haka al'ummar yankin sun bayyana cewa alkaluman wadanda suka mutu a hadarin ya karu zuwa 236, inda kuma ake ci gaba da jinyar wasu da dama a asibitoci daban-daban da ke Maiduguri fadar gwamnatin jihar. Shugaban karamar hukumar Kalabalge na rikon kwarya Alh Babagana Malarima wanda ya tabbatar da karuwar alkaluman wadanda suka mutun, ya ce ya zama dole a taimaka musu da kudaden  da iyalan da suka rasa 'yan uwansu da kuma wadanda suka jikkata  za su yi amfani da su domin tallafawa rayuwarsu. 

Wasu daga cikin al'ummamomin kuma sun bayyana damuwa kan yadda gwamnatoci ba su  mai da hankali ga abin da ya faru akansu ba, inda ko tawagar gwamnatin Tarayya ba ta zo ta duba wajen da abin ya faru ba iya kacinsu Maiduguri fadar gwamnatin jiha. Yanzu haka dai babban abin da ya ke damun wadannan bayin Allah shi ne karancin ruwan sha da kuma hanyoyin da za a fitar da marasa lafiya zuwa asibitoci ko kuma a samar musu da asibitin tafi da gidanka don agajin gaggawa kamar yadda wasu daga cikin al'ummar garin suka bayyana. 

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin Najeriya bata ce komai kan bukatar biyan diyyar ba. Tuni dai kwamitin bincike da rundunar sojojin Najeriya ta kafa wanda ya kunshi kwararru daga cikin rundunar suka isa Maiduguri da nufin fara binciken musabbabin wannan hadari da sojoji suka bayyana a matsayin tsautsayin yaki abin da  jama'a ke bayyana fatan za a fito da hanyar kaucewa afkuwar irin wannan hadari anan gaba.