1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar kawo karshen rikicin Ukraine

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 1, 2017

Shugaban kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya bukaci Rasha da ta yi amfani da tasirin da take da shi a kan 'yan awaren gabashin Ukraine, domin tabbatar da gaggauta kawo karshen rikicin kasar.

https://p.dw.com/p/2WorK
Shugaban kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg
Shugaban kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg Hoto: picture-alliance/abaca/J. Abdulkhaleg

Stoltenberg wanda ya bayyana cewa kungiyar ta NATO za ta ci gaba da goyon bayan Ukraine, ya ce bisa kiyasin da kungiyar tsaro da hadin kan Turai OSCE ta yi, akwai matsaloli na karya ka'idojin yarjejeniyar tsagaita wutar da bangarorin biyu suka cimma sama da 5,600. Faga bisani ya bukaci bangarorin biyu da su gaggauta komawa kan tanade-tanaden yarjejeniyar birnin Minsk da suka cimma a shekarar da ta gabata. Kiran nasa na zuwa ne a dai-dai lokacin da rahotanni ke nuni da cewa sabon fada ya barke a yankin na gabashin Ukraine.