1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar sasanta rikicin Siriya a siyasance

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 11, 2017

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ba za a iya kawo karshen yakin kasar Siriya ba, har sai an yi mafani da tafarkin siyasa wanda al'umma Siriyan ke muradi.

https://p.dw.com/p/2XPAi
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio GuterresHoto: Reuters/S. Keith

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniyar Antonio Guterres ne ya bayyana hakan a birnin Santanbul na kasar Turkiya yayin wata tattaunawa da ya yi da shugaban Turkiyan Recep Tayyip Erdogan. Wata sanarwa da aka fitar bayan tattaunawar tasu ta nunar da cewa, Guterres ya kuma nuna farin cikinsa dangane da abin da ya kira nasarar da aka samu a tattaunawar da aka yi tsakanin gwamnatin Siriyan da 'yan adawa a kasar Kazakhstan karkashin jagorancin Turkiya da Rasha da kuma Iran. A wani labarin kuma dakarun 'yan tawayen Siriyan da kuma na Turkiya da ke mara musu baya sun samu nasarar shiga garin al-Bab na Siriya, inda a fafatawar da suka yi a kokarin kwace iko da garin daga hannun kungiyar IS, sojan Turkiyan guda ya rasa ransa.