1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar shata yankin da babu fada a Siriya

May 4, 2017

Gwamnatin Siriya ta goyi bayan shawarar Rasha ta shata yankunan da za'a hana fada a cikin su a cikiin Siriya a wani mataki na takaita fadan da ke wakana a kasar.

https://p.dw.com/p/2cNvi
Syrien Tabqa SDF Kämpfer
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Syrian Democratic Forces

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan yace shirin shata wasu yankuna da za'a hana fada a cikinsu a Siriya wanda ya sami goyon bayan Rasha zai taimaka matuka wajen kawo karshen yakin basasar da aka shafe shekaru shida ana yi a kasar.

Erdogan wanda ya tattauna shirin da shugaban Rasha Vladimir Putin a ranar Laraba ya baiyana fatan cewa idan aka aiwatar da shirin zai rage da kimanin rabi yawan fadan da ke wakana a kasar ta Siriya.

Turkiyya da Rasha dai sun sha samun sabanin ra'ayi a kan yadda za'a shawo kan rikicin inda Moscow ke goyon bayan shugaba Bashar Al Assad yayin da Ankara ke kokarin ganin ya sauka daga karagar mulki.