1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukin cika shekaru 25 da kafa kungiyar kwadago ta Solidarity a kasar Poland

Mohammad Nasiru AwalAugust 28, 2005

Kungiyar ta taka muhimmiyar wajen kawad da mulkin kwaminisanci a kasashen gabashi da tsakiyar Turai.

https://p.dw.com/p/Bva9
Lech Walesa tsohon shugaban Poland
Lech Walesa tsohon shugaban PolandHoto: AP

“A karshe dai mun samu kungiyar ma´aikata mai zaman kanta. Muna da ´yancin yin yajin aiki kuma nan ba da dadewa ba zamu nemi karin ´yanci.”

Lech Walesa kenan lokacin da yake yiwa ma´aikatan kamfanin kera jiragen ruwa na Danziger Lenin jawabin cimma burin su a ranar 31 ga watan agustan 1980. Hakan dai ya biyo bayan yajin aiki da jerin zanga-zangar da ´yan Solidarity suka shafe makonni da dama suna yi ne wanda a tsakiyar watan agusta ya rikide ya zama wani yajin aiki na gama gari. Miliyoyin leburori da ma´aikatan gwamnati a fadin kasar ta Poland sun shiga wannan yajin aiki don neman a kyautata yanayin aiki tare da samar da kayan abinci.

Abin da ya haddasa wannan yajin aikin kuwa bai taka kara ya karya ba. Hakan ya samu ne bayan da gwamnatin kwaminis ta kara farashin nama a wurin cin abincin ma´aikatan kamfanin na Danziger sannan ta kori wata ma´aikaciya wadda ta nuna adawa da karin farashin. Hakan ya sa dubun dubatan ma´aikata sun shiga yajin aiki duk da fargabar barkewar wata arangama da gwamnati wadda shekaru 10 baya ta murkushe wata zanga-zangar da karfin tuwo.

To sai dai masu shirya yajin aikin sun fara ganin alamar samun nasara bayan da gwamnati ta biyan bukatunsu da suka hada da ´yancin fadar albarkacin baki da sakarwa kungiyoyin ma´aikata mara dake kunshe cikin yarjejeniyar Danziger.

To amma abubuwa sun dauki sabon salo a cikin watan fabrairun 1981 lokacin da aka zabi tsohon ministan tsaro Janar Woyciech Jaruzelski a matsayin shugaban gwamnati, sannan a watan desamban wannan shekara ya janye ´yancin da aka ba ma´aikatan sannan ya kafa dokar ta baci ta tsawon shekaru 2 a fadin kasar ta Poland. Gwamnati ta tsare ´yan adawa da magoya bayan kungiyar ´yan Solidarity ciki har da Lech Walesa wanda aka yiwa daurin talala a gidanshi har zuwa karshen 1982 da shugaban kungiyar mawallafa na kasar Wladyslaw Bartoszewski, wanda a cikin shekarun 1990 aka ba shi mukamin ministan harkokin wajen Poland.

Kungiyar ta Solidarity ta ci gaba da gwagwarmaya a boye, sannan a 1988 wata guguwar canji ta kada cikin kasar sakamakon tashe tashen hankula da gwamnati ta kasa kawo karshen shi. Hakan ya tilastawa shugaban gwamnati Jaruzelski shiga tattaunawa da ´yan adawa sannan a karshe aka gudanar zaben gamagari. A 1990 an zabi Lech Walesa a matsayin shugaban kasa. Amma ba a dade ba sai Solidarity ta fara fuskantar barazanar rushewa. Domin jerin canje canjen da ta fara aiwatarwa a cikin Poland ya rage mata farin jini da tasiri a cikin kasar. Shi ma Walesa ya fara shan suka dangane da ra´ayin sa na rikau abin da ba´a sake zabensa a matsayin shugaban kasa ba a 1995.

Yanzu haka dai shekaru 25 bayan kafa ta, Solidarity ba ta da wani angizo na siyasa to amma tana ci-gaba da aikin ta a matsayin kungiyar ma´aikata mai membobi kusan miliyan daya sabanin a da lokacin da take tinkaho da membobi sama da miliyan 10. Duk da haka dai Walesa ya ce kungiyar ta ba da gagarumar gudummawa wajen sake hade Jamus da kuma kawad da tsarin mulkin kwaminisanci a Turai.