1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukin finafina Afirka Fespaco a Wagadugu

March 19, 2009

Burin bukin na bana shi ne don jaddada muhimmancin al´adun gargajiyar Afirka a wani mataki na bunƙasa harkar yawon buɗe ido a nahiyar

https://p.dw.com/p/HFE8
Fespaco a Wagadugu, Burkina FasoHoto: DW/Christine Harjes

A farkon wannan wata na Maris aka gudanar da bukin nuna finafinan Afirka wato Fespaco karo na 21 a Wagadugu babban birnin ƙasar Burkina Faso. Bukin wanda a bana ya cika shekaru 40, an yi shi ne ƙarƙashin taken "Finafinan Afirka, yawon buɗe ido da kuma bunƙasa al´adun gargajiyar nahiyar Afirka. Manufa dai a nan ita ce jaddada muhimmancin al´adun gargajiyar Afirka da zumar janyo hankulan masu yawon shaƙatawa zuwa wannan nahiya.

To sai dai wani mai haɗa finafinai ɗan ƙasar Mauritaniya Abderamane Cisako wanda fim ɗinsa mai suna "Heremakono ya ci kyautar Yennenga a shekara ta 2003 ya ce wasu ƙasashe sun shafe shekaru goma ba tare da shirya fim ko da guda ɗaya ba yayin da waɗanda Allah Ya ɗigawa garinsu madara sun ka shirya fim bayan shekaru uku.

Matsalar rashin kuɗi da kuma rashin kulawa daga shugabannin siyasa na daga cikin abubuwan dake hana wannan harka bunƙasa a nahiyar ta Afirka. Amma bisa ga dukkan alamu hakan ka iya canzawa nan ba da jimawa ba, domin wasu gwamnatocin kamar ta Nijer sun ƙuduri aniyar taimakawa masu shirya fina-finai a ƙasashensu da zumar bunƙasa al´adun gargajiya.


Mawallafi: Mohammad Awal

Edita: Tijani Lawal