1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukin Kirismeti a birnin Bethlehem

December 25, 2005
https://p.dw.com/p/BvF8

A kuma can birnin Bethlehem dubban masu ziyarar ibada ciki har da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas wanda musulmi ne, suka halarci bukin holimass na Kirismeti. Babban Bishop din birnin Kudus Michael Sabbah yayi amfani da wannan dama don yin kira ga Isra´ila da ta kawad da katangar nan da ta gina wadda ta raba yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan. Bishop din ya yi wa Mahmud Abbas tarba ta zaman lafiya. Abbas dai shi ne shugaban Falasdinawa da ya halarci zaman addu´o´in na farko a cikin shekaru 5. Dukkan maziyarartan dai sun shiga Bethlehem ne daga Birnin Kudus inda a dole suka ratsa ta wani wurin bincike dake tsakanin ganuwar da Isra´ila ta gina don hana kutsen Falasdinawa ´yan gwagwarmaya.