1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukin rantsar da Medvedev

Sambo Othman ShuaibuMay 7, 2008

Rantsar da sabon Shugaban ƙasar Rasha a Moscow

https://p.dw.com/p/Dw6E
Bukin rantsar da Dmitri MedwedewHoto: AP

Da safiyar Larabar nan ce aka gudanar da bukin mika mulki da rantsar da sabon shugaban ƙasar Rasha Dmitry Medvedev.Inda kuma bayan kammala karɓar rantsuwa nan take ya naɗa tsohon shugaban kasar Vladamir Putin a matsayin firayin minisansa.

" Na yi alƙawarin tafiyar da wannann mukami na shugaban tarayyyar Rasha.Zan kare tare da mutunta 'yancin da ikon kowane ɗan ƙasa .Zan kiyaye kuma zan yi biyayya ga tsarin mulkin Rasha.Zan kare cikakken 'yancin da mulki da tsare mutuncin Tarayyar Rasha tare da yiwa al'ummar ƙasar aiki na hakika da gaskiya. "

Sababon shugaban Russia Dmitri Medvdeved ke nan lokacin da yake karbar rantsuwa a gagarumin bukin da aka gudanar a fadar shugaban kasar da aka yiwa lakani da Gold leaf Great Palaceda ke kremlin. Medvedev mai shekaru 42 a duniya ya sami dare kujerar shugabancin kasar ta rusha ne bayan nasarar da ya samu a zaben kasar da aka gudanar a ranar biyu watan maris na wannan shekarar,zaɓen da 'yan kallo masu zaman kansu a ƙasar, suka ƙalubalanta.

Tsohon shugaban ƙasar Vladamir putin shi ne ya fara buɗe bukin da ya sami halarcin manyan jami'ain ƙasar Rashan sama da dubu biyu(2000) .A jawabin da ya gabatar Putin ya yi kira ga sabon shugaban ƙasar da 'yan majalisarsa da su cigaba da ga inda ya tsaya a lokacin da ya ke kan gadon mulki.ya kuma cigaba da cewa:

" Shekaru takwas da suka wuce ,lokacin da na yi rantsuwa da tsarin mulkin Rasha karo na farko , na yi alƙawarin tafiyar da aiki na bisa gaskiya ba kuma tare da rufa-rufa ba ,na kuma yi alkawarin biyayya ga ƙasa ta da al'ummar ta;a duk tsawon wannan lokaci ban karya wannan alƙawari ba.Ko da ya ke a yanzu zan ajiye wannan mukami nawa ,amma zan ci gaba da yiwa ƙasata aiki.Wannan abu ne da na ke daukarsa babba da ke kaina a matsayi na ɗan kasa.Zan kuwa riƙe wannan nawuyi a duk tsawon rayuwata."

Da ya ke jawabi bayan kammala karɓar rantsuwa sabon shugaban ƙasar Rasha Dmitry ya bayana naɗa tsohon shugaban ƙasar Vladamir Putin a matsayin Firayiminista.Haka kuma ya sha alwashin fuskantar gagarumin nauyin da ke gabansa a yanzu tare da neman goyon baya da hadin kan al'ummar ƙasar domin cimma nasara. Ya kara da cewar:


" Wajibi ne mu tabbatar da ganin tsakanin al'ummar mu a mutunta tsarin dokokin ƙasa, an kuma kawar da yanayin nan inda take dokoki ya zama ruwan dare tsakanin mu, saboda hakan ya na samun cigaba irin na zamani.samin tsarin mulki mai ma'ana shi ne sharadin farko na samun bunƙasar tattalin arzikin ƙasa da kyautata rayuwar jama'a.Shi ne kuma sharaɗin farko na yaƙi da ayyukan cin hanci da rashawa."

Shugaban wanda wannan shi ne karon farko da zai riƙe wani muƙamin siyasa ,ya gaji shugabnci mai tashen kan bunƙasar tattalin arziki ta furkar makamashi ,a kuma dai dai lokacin da ƙasar Rusha ta rattaba hannu a kudrin kasuwancin makamashin Nukiliya da Amurka. Lamarin da zai bata damar kutsawa kasuwannin da Ƙungiyar Tarayyar Turai da Amurka su ka mamaye.