1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukukuwan Easter a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya

Al-Amin Suleiman Mohammad/ KSMarch 25, 2016

Bayan da aka samu sauki kan kalubalen tsaro a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya, Kiristoci da dama ne ke gudanar da bukukuwan Easter a mujami’unsu tare da iyalansu sabanin yadda a baya suke yi a gidajensu.

https://p.dw.com/p/1IK2R
Pfingstkirchen in Afrika
Hoto: AP

Bukuwan Easter wanda aka fara daga ranar Jumaar nan zuwa ranar Liltinin sun kasance masu matukar muhimmanci ga mabiya addinin kirista inda suke zuwa majamiu don yin adduoi. A shekarun baya-bayan nan dai mabiya addinin krista na gudanar da bukuwan ne cikin zullumi da fargaba saboda yadda hare-hare na bindiga da kuma na kunar bakin wake suka yawaita a wuraren ibada musamman a yankin Arewacin Najeriya.

Bugu da kari yanayin ya tilasta wa Kiristoci kasa zuwa wuraren bikin Easter inda wasu ke zuwa wasu garuruwa da ke da zaman lafiya yayin da wasu kuma kan kasa zuwa mujamiu don yin addu'oi kamar yadda aka saba yi musamman a jihohin Borno da Yobe, inda rikicin Boko Haram ya tsananta.

Bikin Easter cikin walwala sabanin shekarun baya

Anschläge auf Kirchen in Nigeria Afrika ARCHIV
A baya majami'un sukan kasance ba masu bukuwan EasterHoto: picture-alliance/dpa

Sai dai bikin Easter na wannan shekarar na gudana cikin lumana da kwanciyar hankali a jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya ba kamar yadda ya faru a baya ba in ji Evangelist Musa Misal shugaban matasa Kiristoci na shiyyar.

''Sai dai an tsaurara matakan tsaro a wuraren da za’a yi bukukuwan tare da sa ido don magance duk wani hari na bazata ko na kunar bakin wake da ake samu lokaci zuwa lokaci.''

A na sa bangaren Mark Amani shugaban kungiyar kananan kabilu na Arewacin Najeriya cewa ya yi.

''Duk da yadda ake bikin cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali bukin ya zo lokacin da jama'a ke cikin matsatsin tattalin arzikin kasa.''

Shugabannin mabiya addinin kirista dai sun nemi mabiyan su yi amfani da darussan da ke kunshe a bikin na Easter. Mr Julius Josef na cikin shugabannin da ke neman a yi amfani da darussa da bikin Easter ya koyar.

Yanzu haka dai shugabannin alumma da na siyasa na jaddada kira ga al'umma da su zauna lafiya su kuma so juna, inda yanzu haka wasu Musulmai a wasu sassan yankin Arewa maso Gabashin Najeriya na gadin masu bukukuwan Easter don tabbatar da cewa an yi bikin lami lafiya.