1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bulgaria da Libya zasu bude asusun taimakawa yara masu kanjamau a Libya

December 23, 2005
https://p.dw.com/p/BvFL

Kasashen Bulgaria da Libya,sun amince kafa asusun taimakon yara da suka kamu da cutar kanjamau a kasar ta Libya,inda yanzu haka take tsare da wasu maaikatan jiyya 5 yan kasar Bulgaria da suke fuskantar hukuncin kisa bayan yiwa yaran allurar kwayoyin cutar ta kanjamau.

Wannan sanarwar ta zo kwanaki biyu,kafin maaikatan jiyyar su 5 da kuma wani likita Bapalasdine zasu baiyana gaban kotun koli na Libya inda zasu daukaka kara game zargi da akeyi masu na sakawa yara marasa lafiya a asibitin Benghazi su fiye da 400,jini dake dauke da kwayar cutar HIV da gan gan.

Sun amince kafa asusun ne a wata tattaunawa ta kwanaki 2 da sukayi a birnin Tripoli tsakanin jamian kasashen 2 da kuma wakilai na hukumar turai,Amurka da Burtaniya.

Dukkan bangarorin sun amince da asusun domin taimakawa iyayen yara 426 da suke dauke da cutar,wadanda tuni 50 daga cikinsu sun rigaya sun rasu.

A halin da ake ciki kuma shugaban kasar Bulgaria ya sanar cewa ba zai kashe kudi wajen nemawa wadannan malaman jiyya yancinsu ba ,saboda a cewarsa yin hakan kamar amincewa ne da wannan laifi da ake zarginsu da shi.