1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bundestag ta yi muhawara kan rikici da Iran.

January 26, 2006

Majalisar dokokin Bundestag ta taryyar Jamus, ta yi wata muhawara a kan rikicin da kasashen yamma ke yi da gwamnatin kasar Iran, game da batun makamashin nukilyanta.

https://p.dw.com/p/Bu26
Majalisar Bundestag.
Majalisar Bundestag.Hoto: AP

Kwanaki kadan kafin Hukumar kula da makamshin nukiliya ta kasa da kasa ta yi taronta na musamman kan batun makamashin nukilyan Iran da ake ta korafi a kansa, gwamnatin tarayyar Jamus ta ce da alamun za a iya cim ma madafa a kan wannan batun.

Karamin minista a ma’aikatar harkokin waje, Gernot Erler na jam’iyyar SPD ne ya bayyana haka yau a wani taron da Majalisar dokoki ta Bundestag ta yi don tattauna wannan batun. Jami’in ya kara da cewa, kasar ta Iran dai ta fara nuna sassauci ga shawarar da aka gabatar mata ta azurta sinadarin Ureniyum dinta ne a kasar Rasha. Mahukuntan kasar Iran dai sun nuna alamun amincewa da shawarar Rashan, inji karamin ministan. Tsohon ministan tsaro na tarayya, Rupert Scholz, ya janyo bacin ran `yan majalisar, yayin da ya bukace su da su mai da hankalinsu a kan tattauna batun kera makaman nukiliyan Jamus, ta yin la’akari da barazanar da Iran za ta kasance musu.

An dai kira wannan taron a majalisar dokokin Bundestag ne, saboda bukatar yin haka da jam’iyyar adawa ta Greens ta yi, don kamar yadda ta bayyanar, a san irin matakan da za a dauka idan al’amura suka tabarbare. A zaihir dai, jam’iyyar ta ce ba ta ga wani abin aibu ga matasyin da Jamus ta dauka a kan rikicin makaman nukiliyan da ake yi da Iran ba. Sai dai, abin da ya bata wa wasu jami’anta rai shi ne, kin cewa uffan da shugaban gwamnati tarayya Angela Merkel ta yi, a lokacin da ta gana da shugaba Jacques Chirac na Faransa a ran litinin da ta wuce, dangane da barazanar da ya yi, na yin amfani da makaman nukilyansa, wajen afka wa duk wata kasar da za ta yunkuri kai wa Faransan harin ta’addanci. Kamar yadda shugaban reshen jam’iyyar a majalisar dokoki Jürgen Trittin ya bayyanar:-

„Tun da jawabin ba daidai ba ne, na sa ran cewa Malama Merkel za ta takalo wannan batun a birnin Paris, don ta bayyana bambancin da akwai tsakaninmu a kann wannan batun. Da hakan dai zai fi muhimmanci, a nawa ganin. Kin hakan da kika yi dai, malama Merkel, ina ganin wani babban kuskure ne.“

Da yake mai da martani, Ruprecht Polenz, dan jam’iyar CDU mai kula da manufofin harkokin ketaren jam’iyyarsa, ya ce shugaba Chirac bai ambaci Iran a cikin jawabinsa ba. Bugu da kari kuma, ziyarar da Angela Merkel ta kai a Paris na nuna hadin kan kasashen Faransa da Birtaniya da Jamus a matsayin da suka dauka na tattaunawa da Iran. Jami’in dai ya zargi jam’iyyar ta Greens ne da yunkurin haddasa wani sabani tsakani gwamnati da jam’iyyun adawa:-

„Ni ma ina goyon bayan ra’ayin kaucewa daga yin barazana da karfin soji. Amma ina kuma ganin cewa, bai kamata a susa wa Iran inda yake yi mata kaikayi ba. Mahukuntan Teheran ba sa bukatar wannan dawainiyar.“

A cikn jawabinsa, ministan tsaro Franz-Josef Jung, ya yi kira ne ga kasashen Yamma da su yi amfani da duk wasu hanyoyin zabin da akwai –wato har da na karfin soji – wajen tattauna wa da Iran a kan wannan batun.

Ra’ayoyin `yan majalisar dai sun bambanta, a kan matsayin da Amirka ta dauka, na kai karar Iran gaban kwamitin sulhu na Majalisar dinkin Duniya. A ganin Wener Hoyer, dan jam’iyyar FDP a majalisar:-

„Zai kasance wani gagarumin cikas ne ga gamayyar kasa da kasa, idan aka kai batun ga kwamitin sulhu, aka yi ta dogon turanci ba tare da cim ma wata madafa ba, sa’annan a karshe a sake mika shi ga IAEA. Ba za mu iya dai daukar nauyin wannan cikas ba. Sabili da haka ne ya kamata, a tattaunawar da za a yi da mahukuntan biranen Moscow da Beijing, a ga cewa an cim nasara, fiye da ta shawo kansu kawai su kaurace wa ka da kuir’a a kwamitn sulhun.“

A halin yanzu dai, Peking na watsi ne da batun sanya wa Iran takunkumi; yayin da Moscow kuma, ke yi wa Iran tayin azurta Yureniyum dinta a kasar Rashan, karkashin wani shirin hadin gwiwa tsakanin masana kimiyyan kasashen biyu. Ita dai gwamnatin tarayyar Jamus na marhabin da wannan shawarar ta Rasha. Amma duk wata nasarar da za a iya samu a kan wannan batun, za ta dogara ne kan irin hukuncin da kwamitin zartarwa ta Hukumar Kula da Makamshin Nukiliya ta kasa da kasa zai yanke, a taro na musamman da zai yi a mako mai zuwa.