1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bunkasa noman ban ruwa a Burkina Faso

March 26, 2013

Burkina Faso na yankin Sahel da ke da zafin rana da ƙarancin ruwa, amma duk da haka tun a shekarun 1990 ya kamata a ce ta ninka yawan amfanin gonar da take samu.

https://p.dw.com/p/181my
Brukina-Faso-Tröpfchenbewässerung Paprika bei Ouagadougou Burkina Faso möchte zum Agrar-Exporteur aufsteigen. Seit den 1990er Jahren konnte Burkina Faso seine landwirtschaftliche Produktion verdoppeln. Vor allem durch verbesserte Bewässerungsmethoden ist weiteres Wachstum möglich, sagen Experten. Entscheidend ist zudem der Zugang zu Märkten. Ein Ansatz: Bauern vermarkten ihre Produkte gemeinsam in Genossenschaften und können so bessere Preise erzielen. DW/ Peter Hille
Hoto: DW/P. Hille

Ƙasar Burkina Faso bata da ƙarfin tattalin arziƙi kamar sauran ƙasashen yammacin Afirka, kusan mutane milliyan 16 ke zama a wannan yankin na sahel kuma milliyan huɗu daga cikinsu basu da isashen abinci, a dalilin haka ne ma ƙasar ke dogaro da tallafi daga al'ummar ƙasa da ƙasa.

To sai dai ƙwararru sun ce tun a shekarun 1990 ya kamata a ce ƙasar ta riɓanya abunda ta ke samu daga fanin noma kuma har wa yau a shekaru masu zuwa tana iya ƙara yawan abunda take samu a kowace shekara. Shin wannan na nufin cewa Burkina Faso ta kusan zama ƙasar da ke fitar da amfanin gona ke nan?

Cikin ƙarancin ruwa ana samun yawan amfanin gona

Mando Adaye ya kunna injin ruwa, kuma a hankali injin ya fara aiki yana fitar da ruwa zuwa wani wuri da ke ƙarƙashin ƙasa

Bukina Faso Ouagadougou Obstbauer Mando Adayo Burkina Faso möchte zum Agrar-Exporteur aufsteigen. Seit den 1990er Jahren konnte Burkina Faso seine landwirtschaftliche Produktion verdoppeln. Vor allem durch verbesserte Bewässerungsmethoden ist weiteres Wachstum möglich, sagen Experten. Entscheidend ist zudem der Zugang zu Märkten. Ein Ansatz: Bauern vermarkten ihre Produkte gemeinsam in Genossenschaften und können so bessere Preise erzielen. DW/ Peter Hille
Mando Adayé mai lambu a Burkina FasoHoto: DW/P. Hille

Bayan Adaye ya kunna famfon ruwan, ruwan baya zuba kai tsaye kan shukokin ayabansa da mangoro, ruwan ya kan fito ne ta cikin wani ƙaramin tiyon da ke kwance a ƙasa, tiyon dai na da ƙananan ramuƙa.

Adaye ya mallaki wani lambun 'ya'yan itatuwa ne da ke tsakiyar Burkina Faso. Lokacin bazara akan yi zafi sosai wanda ya kan kai maki 35 bisa ma'aunin Celshious. Daga wurin da lambun ya ke zuwa hamadar ta sahel tazarar sao'i biyu ne da mota. Samun ruwa a nan mawuyacin abu ne.

A dalilin haka ne Mando Adaye ya ƙirƙiro wani tsari na tsimin ruwa. A lokacin damina ya kan tara ruwa cikin wani tanki, yanzu a lokacin bazara sai ya yi amfani da tiyo ya baiwa shuke-shuken na sa ruwa, domin baya so ruwan ya janye da sauri ya yi tsarin yadda da kaɗan, da kaɗan ruwan ke zuba kan shukan.

Bukina Faso Ouagadougou Burkina Faso möchte zum Agrar-Exporteur aufsteigen. Seit den 1990er Jahren konnte Burkina Faso seine landwirtschaftliche Produktion verdoppeln. Vor allem durch verbesserte Bewässerungsmethoden ist weiteres Wachstum möglich, sagen Experten. Entscheidend ist zudem der Zugang zu Märkten. Ein Ansatz: Bauern vermarkten ihre Produkte gemeinsam in Genossenschaften und können so bessere Preise erzielen. DW/ Peter Hille
Amfanin gonaHoto: DW/P. Hille

A da dai yakan yi amfani da bokiti ne yayi ban ruwan kuma yakan buƙaci abunda ya fi yawan da yake amfani da shi yanzu

"Na gamsu da wannan tsarin ban ruwan, komai ya daɗa sauƙi, sau ɗaya kaɗai mutun zai kunna Famfo daga nan sai ya koma ka kwanta. A daa dai na kan wahala domin ni kaɗai na kin yin komai da kaina, yanzu ko lokaci guda na gama"

Burkina Faso ta shirya fitar da amfanin gona?

Kilometa 100 daga kudanci, a ma'aikatar noma da ke babban birnin ƙasar wato Ouagadougou Seydina Oumar Traore shine ke kula da fanin noman rani, kuma wannan sashen ne ya tallafawa injin noman ranin da Adaye ke amfani da shi

"Gwamnatin tana neman tsara shirin da zai inganta irin wannan tsari na banruwan haka nan kuma manoma zasu sami irin injinun yin ban ruwan su yi amfani da su, kuma zasu sami aƙalla rangwamen kashi biyu cikin uku"

Bukina Faso Ouagadougou Landwirtschaftsministerium Direktor Bewässerung-Seydina-Oumar-Traor Burkina Faso möchte zum Agrar-Exporteur aufsteigen. Seit den 1990er Jahren konnte Burkina Faso seine landwirtschaftliche Produktion verdoppeln. Vor allem durch verbesserte Bewässerungsmethoden ist weiteres Wachstum möglich, sagen Experten. Entscheidend ist zudem der Zugang zu Märkten. Ein Ansatz: Bauern vermarkten ihre Produkte gemeinsam in Genossenschaften und können so bessere Preise erzielen. DW/ Peter Hille
Ministan noma Seydina Oumar TraorHoto: DW/P. Hille

Ƙasar za ta bada euro milliyan shidda a shekarar 2013 kamar yadda Traore ya bayyana, kuma fatansa shine Burkina Faso ta zama ƙasar da za ta yi kuɗi sosai daga amfanin gona.

"Akwai abubuwan da muka riga muka fara fitarwa aƙalla zuwa ƙasashe maƙota, misali timatir da albasa zuwa Ghana, Najeriya da Côte d'voire, kuma idan har muka mayar da hankali waje inganta wannan tsarin banruwan, na bada gaskiyar cewa zamu iya tura kayayyakinmu a duk faɗin yammacin afirka wata ƙila ma mu sa su a kasuwannin ƙasa da ƙasa"

A yanzu haka dai wurin kashi biyar cikin 100 ne a ƙasar za a iya amfani da shi wajen irin wannan noman. Akwai dammamaki da dama a cewar Stephen Neu, wanda ke wakiltan bankin raya ƙasa ta Jamus KfW

"Burkina Faso na rayuwa kan ƙananan manoma, manyan manoma, a nan babu irin wannan kwangilar kuma a nan babu al'adar sa, a nan basu da yawa musamman idan aka yi la'akari da cewa suna da yauni sosai, kuma al'ummar na girma kowace shekara kan kashi uku da ɗigo biyu cikin 100 kuma filayen basu wani ƙaruwa"

Ƙaramin gona mai yawan albarka

Ɗan kasuwa Laurent Stravato ya ce shi yana mayar da hankali ne kan ƙananan manoma, haifaffen Italiyan yana tsaye ne cikin wani fili mai girma, akwai manyan-manyan tattasai da suka riga suka ƙosa, ya kuma ce muna ƙoƙarin samar da yanayi mai kyau ne wa ma'aikatan kamfanonin raya ƙasa na ƙasa da ƙasa, wato kamfanin da bashi da manufa ta samun riba, wanda dai zai mayar da hankali wajen samar da wannan injin ruwan ga ƙananan manoma.

Bukina Faso Ouagadougou Laurent Stravato Burkina Faso möchte zum Agrar-Exporteur aufsteigen. Seit den 1990er Jahren konnte Burkina Faso seine landwirtschaftliche Produktion verdoppeln. Vor allem durch verbesserte Bewässerungsmethoden ist weiteres Wachstum möglich, sagen Experten. Entscheidend ist zudem der Zugang zu Märkten. Ein Ansatz: Bauern vermarkten ihre Produkte gemeinsam in Genossenschaften und können so bessere Preise erzielen. DW/ Peter Hille
Laurent StravatoHoto: DW/P. Hille

"Wannan ba juyin juya hali ba ne, ƙasashen Gabas Ta Tsakiya, Israila da Jordan da ma  ƙasashen kudancin Turai sun riga sun yi amfani da irin wannan fasaha, amma  a nan yankin Sahel ana amfani da wannan tsarin na ban ruwan ne saboda bai daɗe da zuwa ba"

Stravato yana so yayi iya ƙoƙarinsa ya ga cewa tsarin ban ruwan ya kawo sauyi mai a'ala a tsarin noman Burkina Faso, kuma manoma za su iya riɓanya girbinsu.

Brukina-Faso-Tröpfchenbewässerung Paprika bei Ouagadougou Burkina Faso möchte zum Agrar-Exporteur aufsteigen. Seit den 1990er Jahren konnte Burkina Faso seine landwirtschaftliche Produktion verdoppeln. Vor allem durch verbesserte Bewässerungsmethoden ist weiteres Wachstum möglich, sagen Experten. Entscheidend ist zudem der Zugang zu Märkten. Ein Ansatz: Bauern vermarkten ihre Produkte gemeinsam in Genossenschaften und können so bessere Preise erzielen. DW/ Peter Hille
Lambun tattasai a kusa da birnin OuagadougouHoto: DW/P. Hille

Mawallafa: Peter Hille/ Pinaɗo Abdu Waba
Edita:         Zainab Mohammed Abubakar