1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buratai: Martani kan zargin almundahana

Uwais Abubakar IdrisJune 28, 2016

Babban hafsan sojan Najeriya ya yi jawabi ga 'yan jaridu kan batutuwan da suka shafi yaki ta’adanci da masu satar shanu da kuma batun zarginsa kan cin hanci da rashawa.

https://p.dw.com/p/1JF0z
Nigeria Armee Task Force gegen Islamisten Boko Haram
Hoto: Getty Images/AFP

Wannan zargi na batun mallakar wasu gidaje a Dubai da aka yi wa babban hafsan sojan Najeriyar dai ya kasance mai daukan hankali a Tarayyar Najeriya musamman ganin yadda wannan batu yake ga gwamnati. Abinda ya sanya ma'aikatar tsaro fitar da sanarwa tana nisanta shi da aikata ba dai dai ba, bisa cewa kokari ne na karkatar da hankalin sojojin daga aikinsu.

Ta dai kaishi ga fitowa fili ya amsa cewa lallai gidajen na iyalansa ne. Babban hafsan ya ce mutanen da ke wannan kulle-kulle za su ga bayansu kamar yadda suka shawo kan masu kai hare –hare na Boko Haram, kuma suna nan suna bincike don gano asalin batun.

Dangane da yanayin tsaro a kasar ta Najeriya kuwa, babban hafsan ya ce a bana za su yi bikin ranar soja a gandun dajin Bakura da a ke wa kalon matattara ce ta masu satar shanu da sojojin suka ce suna da alaka da masu kai hare-hare na Boko Haram.

To sai dai ga Dr Hussani Abdu kwararre a harkokin zamantakewa da ci gaban kasa ya bayyana wasu daga dalilan da ke sanya Najeriya fuskantar wadannan matsaloli.

Da yake bayani a game da ‘yan matan Chibok da ya zuwa yanzu bayan gano biyu daga cikinsu a kwanakin baya babu wani labari. Janar Buratai ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ceto duk wadanda aka sace.

Abin jira a gani ko wadannan bayanai za su kwantar da kurar zargin da wasu kewa kalon kokari ne na kawar da hankalin babban hafsan da a karkashin jagorancinsa ake samun nasaraori a yaki da ta'adanci a kasar.