1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burin Jamus na samun kujerar dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya

Mohammad Nasiru AwalJuly 26, 2004
https://p.dw.com/p/Bvhl

Wannan dai wani sabon karfin guiwa ne da ´yan siyasar Jamus ke hankoro tun bayan kawo karshen yakin cacar baka, wanda yayi sandiyar sake hade kasar Jamus. Ko shakka babu Jamus na da kima a duniya, musamman idan aka yi la´akari da karfin tattalin arzikinta da kuma gudummawar da take bayarwa a ayyukan samar da zaman lafiya karkshin inuwar MDD. A dangane da haka ne gwamnatin birnin Berlin ke hankoron samarwa Jamus dawwamamiyar kujera a kwamitin sulhu.

Ana iya cewa faduwa ta zo daidai da zama, musamman dangane da garambawul da sakatare-janar Kofi Annan ke son yiwa Majalisar ta Dinkin Duniya. Yanzu haka dai mista Annan ya kafa wani kwamitinm kwararru, wanda zai ba da shawarwari bisa manufar da aka sa a gaba kafin nan da farkon watan desamba. Hakan dai kamar yadda gwamnatin tarayya take fata, ka iya kai ga tattauna batun baiwa Jamus kujerar dindindin a kwamitin sulhu. To sai dai babu wani wakilin Jamus a cikin wannan kwamiti.

Duk da fatan da takre yi kuwa bai kamata gwamnatin Jamus ta yi watsi da aihin halin da ake ciki ba. Domin kuwa zai zama wani abin mamaki har in Jamus ta samu yawan kuri´un da take bukata don cimma wannan manufa. Dole sai kasar ta samu yawan kuri´u da ya kai biyu bisa uku na wakilan kwamitin tare da samun kuri´u daga dukkan zaunannun membobi 5 na kwamitin sulhu. Kuma duk da cewa Jamus tana ba da gudummawa daidai-wadaida to amma watakila abin da zata samu ba zai wuce yabo daga sauran kasashe ba. Domin ba´a bayar da kujerar dindindin a kwamitin sulhu kamar lambar yabo.

A nan dai batun iko wato hawa kujerar naki ake. Sau da yawa kuwa ana kasa zartas da kuduri a kwamitin sulhu, saboda daya daga cikin kasashen dake da kujerun dindindin wato Amirka, Rasha, Britaniya, Faransa ko China ta hau kujerar naki. Misalai kuwa a nan suna da yawa, na bayaa-bayan nan kuwa shine kudurori akan Isra´ila, Chechniya da Iraqi. Hakazalika wata kasa kamar Amirka, wadda ba ta samu goyon bayan MDD a yakin da ta yi da Iraqi, ba zata taba yarda a ba wata kasa da ta nuna adawa da wannan yaki, kujerar dindindin a kwamitin sulhu ba.

Muhawwarar da ake yanzu dai shi ne yadda za´a fadada kwamitin sulhu ba tare da ikon hawa kujerar naki ba. To muddin an yi haka kasashe kamar Japan wadda ke ba da kaso na biyu mafi yawa a MDD, ita ma zata bi sahun Jamus wajen neman dawwamammiyar kujera a kwamitin. Wasu kasashen nahiyar Afirka da Latunamirka ma na muradin samun wannan kujera.

Shi yasa yawan kasashen dake goyon bayan Jamus kayyadaddu ne. Watakila hakan Jamus ka iya cimma ruwa idan aka fadada kwamitin sulhu da kasashe masu yawa. Hakazalika kasashe kamar Indiya da Brazil da kuma Nijeriya su ma zasu yi fatan samun wakilci na dindindin a kwamitin sulhun.