1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burin saban Praministan Britania Gordon Brown

June 24, 2007
https://p.dw.com/p/BuHx

Praministan Britania mai jiran gado Gordon Brown, ya bayyana mahimman burin sa, da zaran ya hau karagar mulki.

Ranar labara mai zuwa, a ke sa ran Gordon Brown zai gaji Praminsita Tony Blair, wanda ya alƙawarta yin murabus daga mukƙamin sa, ranar 27 ga watan da me ku ciki.

Bururukan da saban Praministan ya bayyana, sun haɗa da ƙara kyauttata harakokin illimi, da na kiwon lahia,kazalika Brown ya ce ayyanar da talaucin matasa, a matsayin wani babban ƙalu bale da zai yaƙa bil haƙi da gakiya.

Ya yi wanan bayyanai albarkacin taron jam´iyar Labor mai riƙe da ragamar mulki, wanda ya wakana yau a birnin Mancherster.

Ya ɗaya wajen,ya bayyana aniyar gudanar da gyaran fuska, ga jam´iyar Labor, ta yadda za ta sake farfaɗo da kwarjinin ta, wanda masharahanta ke zarginTony Blair da gurbatawa.

Ranar alhamis mai zuwa idan Allah ya kai mu, Gordon Brown zai naɗa sabuwar majalisar miinistocin Britania.