1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burin Wyclef Jean na zama shugaban Haiti

August 6, 2010

Shahararren mawaƙin Amirka, Wyclef zai yi takarar zaɓen shugaban Haiti

https://p.dw.com/p/Oe1s
Wyclef Jean, a lokacin ganawarsa da waɗanda bala'in ambaliyar ruwa ya shafa a Haiti.Hoto: AP

Wyclef Jean, shaharraen mawaƙin hip-hop a ƙasar Amirka ya ba da sanarwar niyyarsa ta tsayawa takararar zaɓen shugaban Haiti, wadda ƙasa ce da talauci yayi wa katutu da kuma har yanzu take fama da raɗaɗin bala'in girgizar ƙasa da ta rutsa da ita a watan Janairun wannan shekara. Mawaƙin, wanda ya ci kyautar fice ta Grammy har sau uku, ya ba da sanarwar haka ne a wani taron magoya bayansa da ya gudana a Port-au-Prince babban birnin ƙasar ta Haiti. A cikin wata fira ta musamman da CNN ta yi da shi, ya nuna dalilinsa na shiga wannan takara. Ko shakka babu Jean wanda tsohon mamba ne na ƙungiyar mawaƙar Fugees zai jefa kansa a cikin takara mai sarƙaƙƙiyar gaske, da kuma aiki mai haɗari. Mutun ɗaya ne dai kaɗai ya taɓa kammala wa'adin shugabancinsa na shekaru biyar a tarihin ƙasar ta Haiti.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Umaru Aliyu