1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina: Gwanmati ta kori Zida daga rundunar soji

Salissou Boukari
December 30, 2016

Shugaban kasar Burkina Faso ya sanar da korar tsofon Firaministan kasar Isaac Yacouba Zida daga rundunar sojojin kasar, bisa laifin tserewa a lokacin da ake zaman lafiya a kasar.

https://p.dw.com/p/2V3uS
Burkina Faso Premierminister Isaac Zida 21.11.2014 Ouagadougou
Tsofon Firaminisran Burkina Faso Isaac ZidaHoto: AFP/Getty Images/S. Kambou

Yayin wani jawabi da ya yi, Shugaba Roch Marc Christian Kaboré na Burkina Faso, ya kuma sanar da shirinsa na yin garan bawul ga majalisar ministocin kasar. Cikin canje-canjen da za a kawo, shugaban zai saki matsayinsa na ministan tsaro, tare da nada wani minista na musamman da zai kula da harkokokin tsaro a kasar a cewarsa, wanda tuni ya nada sabon babban hafsan hafsoshin kasar.

Shugaban na Burkina Faso ya sanar da wani zaman taro da zai gudana a watan Janairu mai kamawa, tsakanin kasashen Nijar, Mali da kuma Burkina Faso, inda za su tattauna kan batun sa ido ga iyakokin kasashen ganin yadda ake dada samun kai hare-haren ta'addanci. A watan Janairu ne dai da ya gabata, Janar Isaac Zida ya samu zuwa wurin iyallansa da ke kasar Canada, bayan da ya samu takardar izini tafiya daga Shugaban kasar Mark Kabore, amma kuma wa'adin ya fice bai dawo ba.