1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burtaniya da Najeriya zasu hada hannu wajen yaki da tarin fuka

January 27, 2006
https://p.dw.com/p/BvAc

Kasashen Najeriya da Burtaniya da kuma dan kasuwar Amurka Bill Gates,sun baiyana aniyarsu ta shirin da zaici dala biliyan 56 domin rage mace mace na mutane miliyan 14 sakamakon cutar tarin fuka cikin shekaru 10 masu zuwa.

Da yake magana wajen taron tattalin arzikin kasashen duniya dake gudana a Davos,Bill Gates ya alkawarta ribanya har sau 3 ,gudumowa da yake bayarwa ga yaki da cutar TB daga dala miliyan 300 zuwa dala miliyan 900 daga nan zuwa shekara ta 2015.

Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo da ministan kudi na Burtaniya Gordon Brown a nasu banagare,sun bukaci yan kasuwa da manyan yan siyasa da suka hallara wajen taron da su goyi bayan wannan sabon shiri nasu.

Shirin da kawadda cutar tarin fuka daga doron kasa,an bullo da shine domin duba wasu sabbin hanyoyi ta hanyar bincike domin yaki da cutar,wadda kasashen Afrika 46 suka aiyana tana bukatar kulawar gaugawa a shekarar bara.