1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burundi: Al'umma na cikin mawuyacin hali

Abdourahmane HassaneApril 26, 2016

Shekara guda bayan da shugaban Burundi Pierre Nkurunziza ya yi tazarce al'ummar kasar na fama da matsaloli bayan da kasashen duniya suka dakatar da bawa kasar tallafi.

https://p.dw.com/p/1Id0B
Burundi Pierre Nkurunziza
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Karaba

Da dama daga cikin 'yan siyasar kasar da kuma jami'an kungiyoyin farar hula sun ficce daga kasar sakamakon yadda suke fuskantar gallazawa daga jami'an tsaro, baya ga irin matsaloli da halin kunci da al'umma ke ciki sakamakon rashin tallafin da kasar ke samu daga kungiyoyin bada agaji da abokan arziki.

Tansania Flüchtlinge aus Burundi
Rikicin siyasar Burundi ya sanya da dama sun yi gudun hijira zuwa kasashe makotaHoto: Reuters/T. Mukoya

Tuni dai al'umma suka fara kokawa game da halin da ake ciki wanda yanzu haka ya fara shafar bangaren ilimi har ma wani dalibi ya ke cewar ''tun lokacin da aka fara yin tashin hankali a kasar dalibai da yawa sun watse, wasu sun hijira a cikin wasu kasashe makobta wasu an kamasu yain da wasu kuma ma sun mutu sakamakon ukubar da aka rika gana musu kuma nan da watanni kadan ne za mu sake komawa karatun amma ga yadda abubuwan suke tafiya.''

Yanzu haka dai tattalin arzikin kasar ta Burundi ya yi kasa da maki 7.5 a shekara da ta gabata saboda halin da kasar ta ke ci abin da ya janyo talauci da fatara da kuma kara hahawar farashin kayan abinci da sauransu a kasar. Wannan ne ma ya sanya wani dan kasar da ke ganin lokaci ya yi da jama'a za su nemawa kansu mafita inda ya ke cewa ''ya kamata mutane su daina tayar da fitina domin a zauna a tattauna don a dakatar da tashin hankali.''

Rikicin da ya biyo bayan tazarcen shugaban kasar dai shi ne ummul aba'isin shiga halin da kasar ta ke ciki kuma tuni kasashen duniya musamman ma wanda ke makota da Burundi din ke fadi tashi wajen ganin an shawo kan wannan matsala domin fidda al'ummar kasar da cikin kangin da suke ciki da nufin samun yin rayuwa cikin walwala kamar sauran mutane.

Burundi Bujumbura Proteste gegen Präsident Pierre Nkurunziza
Mutane da dama na adawa da salon shugabancin Pierre Nkurunziza musamman ma bayan da ya yi tazarceHoto: Heinrich-Böll-Stiftung/Igor Rugwiza