1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bush ya bada sanarwar nadin sabon shugaban CIA---

Jamilu SaniAugust 11, 2004

Yan majalisar datijan Amurka sun soki lamirin nadin da Bush yayiwa Porter Goss a matsayin sabon shugaban´CIA---

https://p.dw.com/p/BvhN
Hoto: AP

Shugaba George W. na Amurka ya bada sanarwar nada Porter Goss dan jama’iyar Repulican a matsayin sabon daractan kungiyar leken asirin Amurka ta CIA,to sai dai kuma bisa ga dukanin alamu nadin da Bush yayi na sabon shugaban kungiyar leken asirin Amurka ta CIA zai haifar da tafka muhawara mai zafin gaske a lokacin da sabon shubaban na CIA zai amsa tambayoyin yan majalisa a game da chanchantarsa wajen rike wanan baban mukami,a lokacin da ya rage makoni kalilan a gudanar da zaben shugaban kasa ranar 2 ga watan Nuwamba mai zuwa a kasar ta Amurka.

Da dama daga cikin yan jama’iyar Democrats sun nuna goyon bayan su ga nadin da Bush yayiwa Goss dan jama’iyar Republican da ya fito daga jihar Florida,wanda kuma jiya talata ya sauka daga kann mukaminsa na shugaban kwamitin tsaro na majalisar datijan Amurka.Koda yake wasu yan majalisar datijan na Amurka sun nuna goyon bayan su ga nadin da Shugaba Bush yayiwa Goss a matsayin shugaban CIA,amman kuma sun soki lamirinsa inda suka ce bai chanchanci a bashi wanan baban mukami ba.

Shi kuwa shugaban jama’iyar Democrats Nancy Pelosi da ya fito daga jihar Califonia,cewa yayi bai kamata a yi amfani da sabani na siyasa wajen zabar sabon shugaban na kungiyar leken asirin Amurka ta CIA ba.

Anasa bangaren Dan majalisar datijan Amurka Jay Rockefeller da ya fito daga yammacin jihar Virginia,wanda kuma ke zaman baban jigo a kwamitin tsaro na majalisar datijan Amurka cewa yayi kuskure ne zabar dan siyasa da ya fito daga kowace jama’iya kann mukamin sabon shugaban kungiyar leken aasirin Amurka ta CIA.

Jay ya kara da cewar koda yake Shugaba Bush nada ikon nada dukanin mutumin da yake so kann mukamin shugaban kungiyar leken asirin Amurka ta CIA,to amman kuma ra’ayin majalisa kann wanan batu nada muhimancin gaske wajen tabatar tsaron Amurka.

Da yake tofa albarkacin bakinsa kann nadin da Bush yayi na sabon shugaban CIA,Pat Roberts shugban kwamitin tsaro na majalisar datijan Amurka,ya nuna rashin jin dadinsa kann irin korafe korafen da aka rika gabatar masa cewar Goss mutumu ne mai son nuna ra’ayinsa na babanci siyasa a fili.

Cikin hirar da gidan talbijin din Amurka na NBC yayi da Roberts ya baiyana cewar a makon farko na watan Satumba mai zuwa yan majalisar dajitan Amurka zasu tattauna,wanda kuma bisa ga dukanin alamu ake ganin yan majalisar datijan Amurka zasu amince da nadin da shugaba Bush yayiwa Poter Goss kann mukamin sabon shugaban kungiyar leken asirin Amurka ta CIA.

A lokacin da Bush ya bada sanarwar nadin Goss kann mukamin shugban CIA,ya baiyana shi a matsayin mutumin da ya san ciki da wajen kungiyar ta CIA,wanda don haka ne ma ya ga ya dace ya nada shi kann wanan mukami.