1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bush ya bukaci Annan ya dauki mataki akan aiyukan jamiansa a Liberia

May 12, 2006
https://p.dw.com/p/Buyk

Kasar Amurka ta bukaci sakatare janar na majalisar dinkin duniya Kofi Annan,daya hanzarta ya dauki mataki akan jamian majalisar,wadanda ake zargi da aikata laifukan ashsha da yara mata a kasar Liberia,yana mai cewa,lokaci yayi da zaa rika kama kasashe da laifukan da yayansu suka aikata.

Jakadan kasar Amurka a majalisar John Bolton,cikin wata wasika da ya aikewa Kofi Annan ya baiyana takaicin gwamnatinsa game da rahoton da wata kungiyar jin kann yara kanana ta fitar,wanda ke baiyana cewa jamian agaji dana majalisar dinkin duniya suna nafani da yara kanana dake sansanonin yan gudun hijira,domin basu abinci da kayan agaji.

Kungiyar ta agaji tace har yanzu halin da yara kanana suke ciki a Liberia bai canza ba tun karshen yakin basasa na Liberia a 1998-2002.

Saboda haka tayi kira ga majalisar dinkin duniya da kungiyoyin jin kai da su inganta horasda jamiansu,tare da gudanar da bincike akan laifukan da rahoton ya sanar.