1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bush ya bukaci fadada ayyukan dakarun NATO a Afganistan

February 15, 2007
https://p.dw.com/p/BuRg

Shugaba George W Bush na Amurka yayi kira ga kungiyar tsaro ta Nato data taimaka wajen cika gibin tsaro dake kasar Afganistan ,ta hanyar tura karin dakarun soji tare da cire kaidojojin aiki da aka sanyawa sojoji da suke kasar a yanzu haka.Bush yayi wannan furucin ne a jawabinsa dake bayyana irin kalubale dake kasar da Afganistan da kuma manufofinsa na samun galaba akan takarun tsohuwar gwamnatin Taliban.Kasashen dake da wakilci a NATO da suka hadar da Jamus dai suna da dakarunsu,daga cikin rundunar kungiyar tsaron dubu 34 dake aikin tsaro a Afganistan,sai dai sun takaita ayyukansu a yankuna da ake da tsaro a kasar.