1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bush ya ce sojin Amurka za su cigaba da zama a Iraqi har bayan waádin mulkin sa

March 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bv4E

Shugaba George W Bush yace Sojin Amurka za su cigaba da kasancewa a cikin ƙasar Iraqi har tsawon shekaru nan gaba. Yana mai cewa ya rage ga gwamnatin da za ta hau mulki bayan ya sauka, ta shawarta lokacin da za ta dawo da dukkanin sojojin gida. Bush wanda ya yi burus da ƙaruwar baƙin jini da sukar lamirin sa da ake yi a dangane da yaƙin, yace ya yi Imani za su cimma nasara. Ya kuma ƙi amincewa da buƙatar da aka yi masa ta sanya sakataren harkokin tsaron Amurkan Donald Rumsfeld wanda ake baiyana cewa shi ne kanwa uwar gami a yaƙin da Amurkan ke jagoranta a Iraqi da Afghanistan da ya yi murabus. Sai dai shugaban na Amurka George W Bush ya yarda da cewa an sami kurakurai a yayin da suka karkata akala ga aikin sake gina ƙasar Iraqi wanda ya ce hakan, shi ne ya baiwa yan tarzoma damar yin ganganko na kai hare haren taáddanci. Bush ya kuma yi watsi da bayanan tsohon P/M Iraqi Iyad Allawi da ke cewa kasar ta fada cikin gararin yakin basasa inda yace a kalla mutane 50 zuwa 60 ne ke mutuwa a kowace a rana a sakamakon dauki ba dadi. A nasa bangaren P/M Britaniya Tony Blair ya amince cewa kasar Iraqi na kan siratsi. Ya danganta afkawa kasar da yaki ga gwagwarmaya tsakanin daidatuwar dimokradiya da kuma ayyukan yan tarzoma