1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bush ya yaba da hukuncin kisa kan Saddam Hussein amma EU ta ce a´a

November 6, 2006
https://p.dw.com/p/BudF

Shugaban Amirka GWB ya yaba da hukuncin da aka yankewa tsohon shugaban Iraqi Saaddam Hussein da cewa wani gagarumin mataki ne a kokarin shimfida demukiradiya a kasar. Bush ya ce hukuncin wani babban ci-gaba ne na maye gurbin mulkin kama karya da mulki na bin doka da oda.

“Shari´ar ta Saddam Hussein gagarumin mataki ne a kokarin da al´umar Iraqi ke yi na kafa wata gwamnati mai bin doka da oda da mutunta hakkin dan Adam. Zamu ci-gaba da taimakawa gwamnatin hadin kan Iraqi a kokarinta na wanzar da zaman lafiya a cikin wannan kasa.”

A jiya wata kotu da Amirka ke goyawa baya ta yankewa tsohon shugaban Iraqin hukuncin kisa ta hanyar ratayewa bayan ta same shi aikata miyagun laifuka. Bush dai bai tabo batun hukuncin kisa da KTT ke nuna adawa da shi ba. A cikin wata sanarwa da ta bayar gwamnatin Finland wadda ke rike da shugabancin kungiyar EU a yanzu ta ce EU na adawa da irin wadannan hukunce hukunce ta kowane fanne, a saboda haka ta na kira da kada a aiwatar da hukuncin kisan da ak yankewa Saddam Hussein. Kotun ta birnin Bagadaza ta same shi da laifin kisan ´yan shi´a 148 a kauyen Dujail a shekarar 1982.