1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bush ya yi alkawarin taimakawa gwamnatin Iraki akan tsaro

November 30, 2006
https://p.dw.com/p/BuZe

Duk da mummunar zub da jini da ake fuskanta a Iraqi shugaban Amirka GWB ya yiwa FM Iraqi Nuri al-Maliki da kuma gwamnatinsa alkawarin ba su cikakken taimako. Bayan ganawar da suka yi a Amman babban birnin Jordan, Bush ya bayyana al-Maliki da cewa jagora ne na kwarai. To sai dai FM na Iraqi ya nuna rashin gamsuwa da yadda har yanzu jami´an tsaro suka kasa shawo mawuyacin halin da ake ciki da yakar masu ta da zaune tsaye ba. Bush da Maliki sun amince akan daukar matakan gaggawa don bawa dakarun tsaron Iraqi horo ta yadda zasu iya karbar jagorancin harkokin tsaro daga dakarun kawance.