1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cacar baka a tsakanin Amirka da Koriya ta Arewa

Ibrahim SaniDecember 6, 2007
https://p.dw.com/p/CYNM

Shugaba Bush ya aike da takarda ta musanman ga shugaba Kim Jong Il na koriya ta Arewa. Wakilin Amirka a tattaunawar warware wannan rikici, wato Christopher Hill ne ya mikawa shugaban wannan takarda.Babu bayanin abinda takardar ta kun sa , to amma zuwanta ya yi dai dai da lokacin da Amirka ke ƙokarin kawo ƙarshen makaman nukiliya na ƙasar ne. Ƙoriya ta arewa dai na daga cikin ƙasashwen na Amirka ta kira shaidanu a shekara ta 2002. A watan oktoba na shekara ta 2006 ne Koriya ta Arewa ta bawa Duniya mamaki, bayan gwajin makaminta na Nukiliya. A shekarar nan dai aka cimma yarjejeniya cewa ƙasar zata halaka makaman na ta, wanda a maimakon hakan Amirka ta ce za ta taimakawa ƙasar da makamashi.