1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Musayar kalamai tsakanin Turkiyya da Jamus

Suleiman Babayo
March 6, 2017

Shugaba Erdogan ya soki Jamus saboda soke tarukan da Turkiya ta shirya yi a Jamus don neman dorewa kan mulki.

https://p.dw.com/p/2YjV0
NATO Gipfel Polen Erdogan Merkel Press Office (BPA)
Hoto: Getty Images/Bundesregierung/G. Bergmann

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiya ya zafafa kalamai kan Jamus game da soke tarukan siyasa da gwamnatinsa ta shirya yi a kasar Jamus, don neman rinjaye a zaben raba gardama na kundin tsarin mulkin kasarsa Turkiya. Wannan gangami an shirya don samun nasara tsakanin 'yan Turkiya kimanin miliyan daya da rabi da ke zaune a Jamus, yayin zaben raba gardama na sabon kundin tsarin mulkin Turkiya da zai kara karfi ga shugaban kasa, da za a yi ranar 16 Afirilu mai zuwa, amma gwamnatin Jamus ta soke tarukan saboda dalilan tsaro. Matakin ya fusata Shugaba Recep Tayyip Erdogan na kasar ta Turkiya wanda ya caccaki mahukuntan Jamus.

 "Na yi tsammanin mulkin 'yan Nazi ya kawo karshe a Jamus, amma har yanzu ana yi. Komai ya fito fili. Daya daga cikin      ministocinma da ya shirya ganawa da ministanku domin neman jawabi. Me ya sa kuka damu. Yanzu na ga irin wannan sanarwa  daga kasar Holland. Dube ku." Inji Shugaba Erdogan na Turkiya.

Türkei Erdogan Rede in Aksaray
Tsamin dangantaka da Jamus bai hana Erdogan yakin neman zabe baHoto: picture-alliance/AP Images/Presidential Press Service/K. Ozer

A daya bangaren ministan kula da harkokin tattalin arzikin Turkiya Nihat Zeybekci wanda yake ziyara a Jamus, ya halarci wani bikin kade-kade a birnin Kolon, kuma ya yi amfani da wannan dama domin neman goyon baya kan gyaran kundin tsarin mulkin kasar domin kara karfi ga shugaban kasa, inda yake cewa:

"kawance da Turkiya na da muhimmancin. Kawayen Turkiya suna amfana da haka. Turkiya za ta shawo kan rikicin da take ciki kuma za mu yi nasara a zaben raba gardama na ranar 16 ga watan gobe na Afrilu"

Ministan na Turkiyya Nihat Zeybekci ya kara da wasu kalaman siyasa inda ya yi tambayoyi da ke cewa, wai shin ma waye ya taimaki kasar Turkiya fita daga matsin tattalin arziki da ta shiga a shekara ta 2001-2002; da wanda ya taimaki kasar zama ta 16 wajen karfin tattalin arziki tsakanin kasashen duniya. Sai mutanen da ke zauren taron suka amsa da cewa Recep Tayyip Erdogan cikin shewa.

Kalaman Shugaba Recep Tayip Erdogan na Turkiya game da kwatanta 'yan siyasan Jamus da 'yan Nazi sun fusata 'yan siyasa wadanda suka ce ya gaggauta neman gafara. Hasali ma a cewar ministan sharia na Jamus Heiko Maas babu wanda zai yarda da hakan. Cem Ozdemir, jagora ne na jam'iyyar kare muhalli a Jamus ya kuma ce:

Deutschland Köln  KoelnArena Auftritt Erdogan Publikum
Erdogan ya saba ganawa da 'yan Turkiya mazauna JamusHoto: Getty Images/V. Rys

"Na yi imanin cewa ya dace mu nuna sanin yakamata wajen mayar da martani. Saboda rama zagi da zagi ba zai magance komai ba. Mu yi tunani idan Erdogan ya rasa samun abin da yake bukata, saboda idan ya samu nasara a zaben raba gardama, Turkiya za ta zama wata masarauta da babu anda zai kula da ita"

A daya bangaren Aydin Ustunel na sashen harshen Turkanci na DW ya ce kalaman suna da nauyi:

"Wata karamar girgizar kasa zan ce, amma na takaitaccen lokaci. Duk kasashen suna bukatar juna, Jamus tana bukatar Turkiya kan 'yan gudun hijira, ita kuma kasar Turkiya tana bukatar Jamus kan tattalin arziki mai muhimmanci"

Kasashen Turai suna kara nuna damuwa kan matakin gwamnatin Turkiya na kame-kame tare da sallamar mutane daga aiki tun bayan yunkurin kifar da gwamnati na watan Yuli.