1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cameron bai samu rinjaye a majalisar Birtaniya ba

May 7, 2010

Babbar Jam´iyar adawa ta Birtaniya ta kasa samu rinjaye da zai bata damar kafa gwamnati.

https://p.dw.com/p/NIhb
Madugun adawan BirtaniyaHoto: AP

Jam´iyar adawa ta Conservetive ta yi nasarar lashe zaɓe 'yan majalisa da ya gudana a jiya ba tare da samun rinjaye da zai bata damar kafa gwamanti ba. A daidai lokacin da aka kusa kammala ƙidaya ƙuri´un da aka kaɗa, madaugun 'yan adawa na Birtaniya wato David Cameron ba shi da tabbacin samun ƙujeru 326 da ake bukata domin jan aƙallar mulki. 

Kujeru 299 ne jam'yar Conservative ta lashe ya zuwa yanzu, yayin da ta Labour ta ke da kujeru 254. Firaminista mai barin gado wato Gordon Brown da jam'iyarsa ta yi asaran kujeru 90, na ci gaba da nuna ƙwarin guywa game da manufarsa ta yin tazarce.  jam'iyar liberal Democrats wacce ta zo ta uku- ake sa ran zata zama raba gardama na tabbatar da jam'iyar da zata jagorancin ƙasar.

Shugaban wannan jam´iya wato Nick Clegg ya bayyana aniyarsa ta haɗewa da jam´iyar Conservative, duk ta rashin tabbacin cewa kwalliyarsu za ta mayar da kuɗin sabulu. Wannan dai shi ne karon farko cikin shekaru sama da talatin da aka kasa samun jam´'iya mai cikekken rijaye a majalisar ta Birtaniya.

Mawallafi:Mouhamadou Awal

Edita: Halimatu Abbas