1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Canada tace zata tsugunad Palasdinawa 50

October 8, 2006
https://p.dw.com/p/Bugw

Hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar dinkin duniya tace tana fatar tsugunarda Palasdinawa kusan 50 wadanda suka tsere daga Iraqi shekaru 3 da suka shige a kasar canada,tana mai baiyana damuwarta game da dubban yan gudun hijira da har yanzu suke makale a Iraqin da Syria da kuma Jordan.

Komishin kula da yan gudun hijra ta majalisar dinkin duniya yace,halinda Palasdinawa yan gudun hijira a Iraqi suke ciki,sai kara muni yakeyi cikin watanni nan.

An kiyasta cewa Palasdinawa kusan dubu 34 ne suke zaune a Iraqi kafin Amurka ta mamaye kasar.

Wakilin hukumar ta yan gudun hijira a Jordan Robert Breen ya fadawa kanfanin dillancin labaru na AFP cewa kasar canada ta amince ta karbi Palasdinawa 50 daga sansanin yan gudun hijira na Ruwaysheed dake bakin iayaka Iraqi.

Kasar jordan wacce ta baiwa palasdinawa miliyan 1 da dubu dari bakwai dac suka tserwa rikicin Israila matsuguni,ta kuam sake karbar wasu Palasdinwa 386 da suka tsere daga Iraqi tun 2003.