1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cece Kuce A Game Da Kalamin Da Ya Fito Daga Bakin Shugaban Kasar Jamus

September 13, 2004

A cikin wata hira da aka yi da shi, shugaban kasar Jamus Horst Köhler ya bayyana cewar zai dauki lokaci mai tsawo da kuma juriya da dagewa a kokarin da ake yi na cike gibin dake akwai tsakanin gabaci da yammacin kasar ta Jamus

https://p.dw.com/p/BvgX
Shugaban kasar Jamus Horst Köhler
Shugaban kasar Jamus Horst KöhlerHoto: dpa

A sakamakon tofa albarkacin bakinsa da yayi a game da halin da ake ciki a gabacin Jamus, a lokacin wata hira da aka yi da shi, shugaba Horst Köhler ya haddasa cece-kuce a siyasar kasa baki daya. Jami’in jam’iyyun the Greens da SPD na zarginsa da yunkurin jefa mutane cikin halin rashin sanin tabbas da kuma yi wa jam’iyyar PDS yakin neman zabe a fakaice. Shi dai shugaban kasa Horst Köhler ya fito fili ne yana mai yin nuni da banbance-banbancen dake akwai a matsayin rayuwa a nan kasar, kama daga arewaci zuwa kudanci da kuma yammaci zuwa gabacinta, kuma duk wani yunkurin da za a yi na kawar da wannan gibi zai haifar da matsalolin da zuriya ta gabata zata sha fama da radadinsu. Amma duk da haka tilas ne a ci gaba da tallafa wa jihohin gabacin Jamus da kudi domin daga matsayinsu daidai da jihohin yammacin kasar. Sai dai kuma wajibi ne kowa-da-kowa ya ba da gudummawa gwargwadon ikonsa. An saurara daga bakin mataimakin kakakin gwamnati Thomas Steg yana mai yin nuni da cewar babban abin da gwamnati ta sa gaba shi ne daidaita matsayin rayuwa tsakanin gabaci da yammacin Jamus kamar yadda daftarin tsarin mulkin kasar ya tanada. Wannan ba wata manufa ce ta siyasa ba, abu ne da ya shafi kowa da kowa. An saurari irin wannan bayanin daga bakin shugaban jam’iyyar SPD kuma kakakinta a majalisar dokoki Franz Münterfering, wanda ya ce ba kawai jihohin gabacin Jamus ne maganar daidaita matsayin rayuwar ta shafa ba har ma da wani bangare na jihohin yammacin kasar. A nata bangaren shugabar 'yan hamayya na Christian Union Angela Merkel ta gabatar da kira ga masu sukan lamirin shugaban kasa Horst Köhler da su saurari dukkan bayanan da shugaban yayi a cikin hirar da aka yi da shi a tsanake kafin su kalubalance shi. Domin kuwa bayanin nasa baya nufin rungumar kaddara da saduda ga wadannan banbance-banbance na rayuwa har abada. Duk wanda ya natsu ya saurari bayanin shugaban kasa Horst Köhler zai fahimci nuni da yake yi game da muhimmancin cike wannan gibi. Amma hakan ba zai samu ba sai da juriya da kuma hangen nesa. Ita ko shugabar jam’iyyar the Greens Angelika Beer ta tunasar ne da cewar alkawururuka na bunkasa da tsofon shugaban gwamnati Helmut Kohl yayi wa mazauna gabacin Turai a zamanin baya ba abu ne da zai samu a cikin kiftawa da Bisimillah ba, kuma ta la’akari da haka babu wani sabon abu a game da kalamin shugaban kasa Horst Köhler akan wannan batu. Matsalar dake akwai ita ce kasancewar ire-iren wannan lafazin zai kara haddasa baraka tsakanin gabaci da yammacin Jamus, musamman a daidai wannan lokaci da kasar ke cikin hali na kaka-nika-yi da matsalolin dake gabanta. Shi dai Köhler yayi alkawarin cewa za a ci gaba da tallafa wa jihohin gabacin kasar ta Jamus har kwanan gobe kuma a saboda haka babu wani dalili na karayar zuci da fid da kauna, ita kuma maganar yi wa PDS yakin neman zabe ba ta taso ba.