1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cece-kuce kan gyara kundin tsarin mulkin Najeriya

Uwais Abubakar Idris/ MABJuly 1, 2016

Majalisar wakilan Najeriya na son yin amfani da rahoton taron kasa da aka gudanar a 2014 a matsayin madogara wajen yi wa tsarin mulki gyaran fuska. Sai dai wasu 'yan siyasa suka ce ba zata sabu ba.

https://p.dw.com/p/1JHV9
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Cece-kuce kan gyara kudin tsarin mulkin Najeriya

Wannan matakin ne daukar hankalin jama’a musamman sanin irin kiraye kiraye na a sake wa Najeriyar fasali da ke kara amo a kasar a yanzu. Dama rahoton taron kasar na 2014 na batun rabon arziki kasa da ma rage wa gwamnatin tsakiya karfi, abubuwan da masu da’awa da aware ke nuna goyon baya a kansa. Sai dai Dr Abubakar Umar Kari na ganin cewa akwai bukatar yin taka tsan-tsan da wannan shawara da majalisar wakilan ta dauka.

Kwamitin gyara tsarin mulki na majalisar wakilan Najeriya ya bayyana cewa za’a yi amfani da rahoton taron kasar ne don ya zama jagora wajen sake fasalin tsarin mulkin. To amma da alamun za’a fuskanci tirjiya ga wasu ‘yan majalisar irisn su Hon Ahmed Baba Kaita da ya ce bafa zasu yarda ba.

Muhammadu Buhari und Atiku Abubakar
Atiku Abubakar na goyon bayan kwaskware Kundin tsarin mulkiHoto: Atiku Media Office

Masu kiraye-kirayen bukatar sakewa Najeriya fasali na kara karfi, musamman tun bayan ambata hakan da tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya yi, bayan nan Farfesa Wole Soyinka ya bi sawu. Ga Dr Abubakar Umar kari na ganin akwai bukatar yin taka tsan-tsan.

‘Yan Najeriya na sanya idanu a kan gyaran tsarin mulki na 1999 wanda so uku kenan ana yunkuri a majlaisar ba tare da samun nasarar ganin kammala shi ba. Za’a sa ido a gani ko a wannan karon na majalisa ta 8 za’a kaiga biyan bukata a aikin da tuni wasu ke kallon kokari ne na sake kashe makudan kudadden kasar a yanayi na matsalolin tattalin arziki.