1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi: Fafutikar sakin Tadjeddine Mahamat

Salissou Boukari
January 18, 2018

Wani kwamiti da ke goyon bayan dan fafutikar nan na kasar Chadi Tadjeddine Mahamat Babouri, da ke tsare a gidan kaso watanni 15 ya shigar da kara a gaban kotun daukaka kara ta neman a sallamo shi.

https://p.dw.com/p/2r7Eb
Tschad Gericht in Dakar Hissene Habre Prozess
Ma'aikatar shari'a ta kasar ChadiHoto: Getty Images/AFP/Seyllou

Tun dai a ranar 13 ga wannan wata na Janairu aka kafa kwamiti a wani mataki na fadada bukatar neman a sallamo dan fafutikar daga tsaron da ake yi masa tun daga tsakiyar watan Satumba na 2016 sakamakon wasu kalamai da ya yi na suka ta shafinsa na Facebook ga shugaban kasar ta Chadi Idriss Deby Itno. A cewar mai magana da yawun kwamitin da aka kafa Jean-Bosco Manga yanzu dai sun shigar da kara domin ganin an sake shi

A cewar kungiyar kare hakin bil-Adama ta Amnesty International, an dauke dan fafutikar Tadjeddine Mahamat Babouri yayin da yake tafiya a tsakiyar titin birnin N'Djamena 'yan kwanaki kalilan bayan da ya wallafa wani bidio na sukar Shugaba Deby, inda ake ci gaba da tsare shi a gidan kaso na Moussoro da ke tsakiyar kasar bayan da ya shafe watanni da dama a gidan kaso na Koro Toro da ke arewacin kasar.